islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Tuba daga barin sa’bo


11517
Surantawa
Idan kazanta da dauda suka yawaita a tufafin sawa, me kake tunani da wannan tufa? To haka ma zuciya take, miye tunanin ka idan zunubbai suka cushe ta,da karancin istigfari da tuba? Lallai mumini baya rasa zunubbai, kuma ba sharadi bane ya zama maasumi, saidai ya zama wajibi ya zama me dimantar tuba da komawa zuwa ga Allah. Kuma zuciyar da ke lefi baya tuba, kamar tufa ne da ba a wanke ta, don haka duk mai son zuciyarsa ta wanku, sai ya dawwama wajen tuba da istigfari.

Manufofin huxubar

Komawa ga Allah (S.W.T)

Shiryar da mutane abisa kyautata alaqarsu da Ubangiji

Barin xebe tsammani da samun rahamar Ubangiji

Huxuba Ta Farko

Haqiqa dukkan yabo ya tabbata ga Allah muna godemasa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawukanmu da kuma munanan ayyukanmu. Duk wanda Allah ya shirye shi babu mai vatar da shi, wanda kuma duk ya vatar da shi babu mai shiriyarsa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai ba shi da abokin tarayya kuma ina shaidawa haqiqa Annabi Muhammadu bawansane kuma manzonsane.

“Yaku waxanda sukayi imani kuji tsoron Allah haqiqanin jin tsoronsa kada ku kuskura ku mutu face sai kuna musulmai” (Al-Imran 102).

“Yaku mutane kuji tsoron Allah wannan da ya halicce ku daga rai guda xaya ya halitta daga jikin matarsa sannan ya yaxa daga su biyun mazaje da yawa da kuma mataye kuji tsoron Allah wannan da kuke yin tambaya (roqo) da shi da kuma zumunci haqiqa Allah ya kasance akanku mai tsaro” (Nisa’i 1).

“Yaku waxanda sukayi imani kuji tsoron Allah ku faxi magana ta daidai, sai Allah ya gyara muku ayyukanku kuma ya gafarta muku zunubanku duk wanda yabi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabo mai girma” (Al-ahzab 70 – 71).

Bayan haka;

Yaku bayin Allah ku sani, haqiqa kowa ne mutum aikin da aka halicce shi dominsa shi ne ibada. Don haka duk abin da ya aikata na alkhairi to sakamakonsa nasa ne, yana jiransa, kamar yadda duk abin da ya aikata na aikin savo to wannan tawaya ce a cikin aikinsa. Kuma cutarwarsa tana komawa akansa kuma zunubi duk inda ya kai da yawa baya cutar da allah da komai, kamar yadda aikin xa’a baya amfanar da shi da komai.

Shin ko mun sani – Ya ku musulmi - cewa zunubai qazantace Manzon Allah (ﷺ) shi ne ya ambace ta da sunan qazanta ya zo a cikin littafin Muwaxxa ta Imam Malik (R.A) cewa Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Duk wanda ya aikata wani abu na irin wannan qazantar, to ya suturce da suturar Allah...”. Koda kuwa mu ba ma ganin wannan qazantar afili, koda kuwa ba ma shaqar warin ta, sai dai ai muna ganin alamun zunuban abisa zukata. Zunubi yana bin bayan zunubi har sai ya lulluve zuciya. Allah (ﷺ) yana cewa:

( كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَى قُلُوبِهِمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ 14 ) [المطففين: 14]

(A’aha ba haka ne ba! abin da suka kasance suna aikatawa dai ya yi tsatsa a kan zukatansu).

Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Haqiqa bawa idan ya yi wani zunubi sai wani baqin xigo ya ya samu akan zuciyarsa, idan kuma ya tuba daga wannan zunubin sai zuciyarsa ta yi haske. Idan kuma ya kama ya qara aikatawa sai baqin ya qaru)”. (Tirmizi).

Waxannan zunuban suna taruwa a cikin zuciyar bawa idan dai har ba’a samu tuba ko istigfari ya biyo bayansu ba har sai zunubin ya cunkushe ta ya lulluve ta gaba xayanta.

Ya ku musulmi idan qazanta ta yi yawa bisa tufafi. kuma aka samu qarancin wanke ta to mai kuke tsammani zai faru? To ita zuciya kwatankwacin haka take duk zuciyar da zunubai suka yi yawa a cikinta tuba yayi qaranci a gareta menene zai faru da ita?

Ya ku musulmi haqiqa mu muna yin zunubi dare da rana, sau da yawa ma wani sai kwanaki da yawa su shuxe bai xaga hannayensa ba, ya tuba ga Allah. Bai roqe shi gafara abisa irin abin da yake aikatawa na zunubai ba. To me kuke tsammani da irin zuciyar wannan?

Tsabtata ta haqiqa ita ce tsabtar zuciya. Tsabtar tufafi ba ta da wani amfani, in har dai zuciya tana gurvace da qazantar zunubi da savon Allah (S.W.T).

Sau da yawa mutum yana iya kasancewa tufafinsa masu tsabta, amma zuciyarsa daga ciki tana cike da dattin qazantar zunubai mai wari, saboda ko wacce rana yana qara mata datti ta hanyar aikata zunubai da kuma rashin tuba da rashin istigfari. Ba shi da wata daraja a karan kansa. Kuma ba shi da daraja a wajen mutane da a ce za su gane haqiqaninsa. Kuma ba shi da wata qima a wajen mahaliccinsa a ranar Alqiyama, ranar da za a tona asirai, ranar da za a fitar da dukkanin abin da zuciya ta voye alhalin babu abin da yake vuya ga Allah komai qanqantarsa.

Ya ku musulmi dukkan mutane suna yin zunubi sai dai bambanci a tsakaninsu akwai wanda yake gaggawa ya tuba gabarin zunubansa ya kawar dasu ya tsarkake zuciyarsa da tuba da istigfari, sannan kuma akwai wanda yake gafala ya rafkana ga barin zunubansa har su ruvanya a cikin zuciyarsa.

Ya ku bayin Allah! qofar neman gafara a buxe take domin mu tsabtace zuqakanmu daga waxancan zunubai waxanda muke aikatawa a kullum. Ya ku bayin Allah mu masu roqon Allah ne mai girma bisa ya karvi tubanmu, domin mu yayewa wannan zuciyar irin nauyaye-nauyayenta, waxanda suka shiga tsakanin mu da samun nutsuwa a cikin rayuwanmu. Ubangiji yana cewa:

( قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَى أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ 53 ) [الزمر: 53]

“Ce da su, (Allah yana cewa) «Ya ku bayina waxannan da suka yi varna ga kawunansu kada ku xebe tsammanin samun rahmar Allah, domin Allah yana gafarta zunubai ne gaba xaya, kuma haqiqa shi mai gafara ne mai jin qai ne”.

Bayin Allah, haqiqa yana daga cikin sunayen Allah maxaukaki akwai «mai gafara, mai karvar tuba», kuma su waxannan sunayen guda biyu masu girma sun qunshi siffar Gafara da kuma karvar tuba, domin shi Allah (S.W.T) yana karvar tuba daga bayinsa, kuma yana yin rangwame dangane da zamiya da sukayi. Allah (S.W.T) ya ce dangane da Annabi Musa sanda ya kashe wani mutum ba tare da niyya ba

( قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي فَاغْفِرْ لِي فَغَفَرَ لَهُ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ 16 ) [القصص: 16]

(Ya ce, ya Ubangijina haqiqa ni na zalunci kaina, ka gafarta min. Sai (Allah) ya gafarta masa, domin shi mai gafara ne mai jin qai).

Ubangiji (S.W.T) ya ce dangane da Annabi Adam:

( وَعَصَى آَدَمُ رَبَّهُ فَغَوَى 121 ثُمَّ اجْتَبَاهُ رَبُّهُ فَتَابَ عَلَيْهِ وَهَدَى 122) [طه: 122]

“Adam ya savawa Ubangijinsa sai ya vace. Sannan Ubangijinsa ya zave shi, ya karvi tubansa, ya shiryar da shi”.

Ubangiji maxaukaki ya ce:

( وَهُوَ الَّذِي يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ وَيَعْفُو عَنِ السَّيِّئَاتِ وَيَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ 25 ) [الشورى: 25]

(Shi ne wanda yake karvar tuba daga wajen bayinsa, kuma yake yin afuwa game da munanan aiyuka).

A cikin wannan aya mai girma, Allah maxaukakin sarki ya bayyana cewa, shi kaxai shi yake karvar tuban bawa idan ya tuba ya bar zunubai da laifuffuka. Ya qara bayyana hakan a wasu wure daban, kamar inda yake cewa:

( أَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ هُوَ يَقْبَلُ التَّوْبَةَ عَنْ عِبَادِهِ وَيَأْخُذُ الصَّدَقَاتِ وَأَنَّ اللَّهَ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ 104 ) [التوبة: 104]

“Shin basu sani ba cewa haqiqa Allah shi yake karvar tuba daga bayinsa kuma shi yake karvar sadaka. Kuma haqiqa shi Allah shi ne mai karvar tuba, kuma shi ne mai yin rahama”. Da faxinsa maxaukaki:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَصُوحًا عَسَى رَبُّكُمْ أَنْ يُكَفِّرَ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ) [التحريم: 8] “Ya ku waxanda suka yi imani ku tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya, tabbas Ubangijinku zai gafarta muku laifuffukan ku”. Da kuma faxinsa (S.W.T):

( وَمَنْ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ) [آل عمران: 135]

“Waye yake gafarta zunubai idan ba Allah ba”.

Da sauran ayoyi masu kama da waxannan.

An karvo hadisi daga Abu Musa, Abdullahi bn Qais al-Ash’ari (R.A) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce, “Haqiqa Allah maxaukaki yana shimfixa hannunsa da daddare domin ya karvi tuban mai yin savo da rana, kuma yana shimfixa hannunsa da rana domin ya karvi tuban wanda yayi zunubi da daddare, har sai lokacin da rana ta hudo daga mafaxarta”. (Muslim)

Haqiqa sakamakon imani da sunayen Allah "Mai gafara" da kuma "Mai karvar tuba" suna bayyana ne ga bawa idan ya zama mai komawa ga Allah ta hanyor qanqan da kai a gare shi, da kuma neman gafara dangane da zunuban da ya gabatar a baya, da kuma rashin xebe tsammani ga samun rahamar Ubangiji maxaukakin sarki.

Ya ku bayin Allah! Lalle ita tuba ga barin dukkan zunubai wajibi ne, wanda kuma ana so ya zama an aiwatar da shi da gaggawa, domin yin jinkirta tuba alamace ta tsiyatar lahira ga bawa, da tavewa, da ma shafewar basira. Allah ya tsare mu.

Ubangiji maxaukaki yana cewa:

( وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَا الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 31 ) [النور: 31]

“Ku tuba zuwa ga Allah baki xaya ya ku muminai ko kwa rabauta”.

Kuma yana cewa,

( اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ ) [هود: 52]

“Ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba zuwa gare shi”.

Yana cewa:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَصُوحًا ) [التحريم: 8]

(Ya ku waxanda suka yi imani ku tuba zuwa ga Ubangijinku tuba nagari).

Don haka waxannan ayoyin dama waxanda suke xauke da ma’anoni irin nasu duka suna nuni abisa wajibcin tuba daga dukkanin aikin savo, domin a cikin su waxannan ayoyin akwai umarni da yin tuba gaba xaya. Malaman Usulul fiqhi suna cewa: Dukkan umarni yana fa’idantar da wajabci ne, sai dai idan wani dalili ya nuna rashin wajibcin.

An karvo daga Abu Huraira (R.A) ya ce: “Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Na rantse da Allah ina neman gafarar Allah da kuma tuba a gare shi a kowanne yini sama da sau saba’in. (Bukhari).

A cikin hadisin da aka karvo daga wani sahabi mai suna Al’agarru xan Yasar Al-muzniy (R.A) ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ya ku mutane ku tuba ga Allah ku nemi gafararsa haqiqa ni ina tuba a kowanne wuni sau xari” (Muslim).

Malamai suka ce, idan bawa ya tuba ya bar wasu daga cikin zunubansa to zance mafi inganci tubansa ya inganta abisa zunubin da ya tuba gabarin yinsa. Amma sauran sunan awuyansa ba za su gushe ba har sai sanda ya tuba.

Kuma ita tuba bata zama ta gari har sai idan ta cika sharuxxa guda uku:

Ya qauracewa zunubin idan yana yinsa.

Sannan ya yi takaicin abin da ya gabata na savawa Ubangijinsa.

Ya yi niyya da gaske ba zai sake komawa ba kan wannan zunubin har abada.

Abin da ya fi fitowa fili ta hanyar dalilai masu qwari a cikin maganganun malamai shi ne, idan bawa ya tuba daga aikata wani zunubi sannan daga baya ya sake komawa ya aikata to wancan tuban nasa na farko ya inganta, sai dai ya sake tuba a karo na biyu. Ba kamar yadda wasu suke cewa; komawarsa ta rushe wancan tuban na farko ba.

Na biyu: Malamai ba su yi savani ba akan cewa tuba ba ta inganta, sai idan an haxata da yin nadama bisa zunubin da aka aikata. Sannan da barinsa idan ya kasance shi mai aikatawa yanayin zunubin.

Yana aga cikin sharuxxan tuba biyan abin da ya kamata a biya, wanda aka yi sakaci a kansa. Misali: Mayar da abin da aka zalunci wani akansa.

An karvo daga Aliyu xan Abi Xalib (R.A) cewa: Tuba ta qunshi abubuwa guda shida:

Yin nadama abisa abin da ya gabata na zunubai

Biyan farillan da aka bari ba a yi su ba.

Da mayarwa wanda aka zalunta abin da aka zalunce da shi.

Kuma ya nemi abokin husumarsa da ya yafe masa.

Yayi takai da kawowa wajen yin xa’a ga Allah kamar yadda ya narke cikin sava masa.

Kuma ya xanxana mata xacin biyayya ga Allah, kamar yadda ya xanxana mata zaqin aikin savo.

Lallai ana son ayi alwala da yin sallah raka’a biyu a yayin tuba, tare da cika sharuxxan da aka ambata a baya, saboda hadisin da Imam Ahmad ya ruwaito daga Aliyu xan Abi Xalib (R.A) ya ce: Na kasance idan na ji hadisi daga Manzon Allah (ﷺ) Allah yakan amfanar da ni shi da abin da ya so. Idan kuma wani ne ya faxa mini hadisi daga gare shi, ina neman ya rantse, idan ya rantse min sai in gaskata shi. Abubakar ya faxa mini wani hadisi, kuma shi Abubakar gaskiya ya faxamin, cewa, ya ji Ma’aikin Allah (ﷺ) ya ce: “Babu wani mutum da zai aikata wani zunubi sannan ya yi alwala kuma ya kyautata alwalarsa, sannan kuma ya yi sallah raka’a biyu, sannan ya nemi gafarar Allah mai girma da xaukaka face Allah ya gafarta masa”.

Abin da yake qara tabbatar da ingancin wannan hadisin shi ne hadisin da Imam Muslim ya ruwaito a cikin ingantaccen littafinsa daga Sarkin Muminai Umar xan Khaxxabi (R.A) daga Annabi (ﷺ) cewa: “Babu wani a cikinku da zai yi alwala ya cika alwalarsa sannan ya ce, "Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Sannan kuma na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, face sai ambuxe masa qoqofin aljanna guda takwas ya shiga ta wacce yake so".

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da aminci su qara tabbata ga shugaban Manzanni, Annabin mu Muhammad da iyalan gidansa da sahabbansa baki xaya.

Bayan haka;

Haqiqa nassoshi na shari’a sun nuna ba za karvi tuban bawa ba yayin da rai ya kai maqoshi, wato ya kai hali na gargara. Da kuma yayin da rana za ta hudo daga mafaxarta. Allah maxaukakin sarki ya ce:

( هَلْ يَنْظُرُونَ إِلَّا أَنْ تَأْتِيَهُمُ الْمَلَائِكَةُ أَوْ يَأْتِيَ رَبُّكَ أَوْ يَأْتِيَ بَعْضُ آَيَاتِ رَبِّكَ يَوْمَ يَأْتِي بَعْضُ آَيَاتِ رَبِّكَ لَا يَنْفَعُ نَفْسًا إِيمَانُهَا لَمْ تَكُنْ آَمَنَتْ مِنْ قَبْلُ أَوْ كَسَبَتْ فِي إِيمَانِهَا خَيْرًا قُلِ انْتَظِرُوا إِنَّا مُنْتَظِرُونَ 158 ) [الأنعام: 158].

(Ba komai suke jira face sai mala’iku sun zo musu, ko kuma Ubangijinka ya zo, kuma sai wani sashin ayoyin Ubangijinka sun zo, to lokacin da wani sashi na ayoyin Ubangijinka zai zo, to a wannan lokacin rai wadda ta kasance ba ta yi imani ba, kafin haka, ko kuma ba ta tsuwurwuci wani aikin alkhairi a cikin imaninta ba, imaninta ba zai amfane ta ba. Ka ce, «Ku saurara haqiqa mu masu saurarawa ne”).

Sashen ayoyin Ubangijinka za su zo musu ne kafin ranar Alqiyama. Kuma yana daga cikin alamomin tashin Alqiyama, kamar yadda al-Imam al-Bukhari ya faxa a cikin tafsirin wannan ayar.

An karvo daga Abu Huraira (R.A) ya ce Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Alqiyama ba za ta tashi ba har sai yayin da rana ta vullo ta mafaxarta, idan mutane suka ganta ayayin sai waxanda suke akan qasa duk su yi imani a sannan to wannan shi ne imanin da wata rai ba zai amfaneta ba matuqar ba ta yi imani ba kafin sannan".(Bukhari)

An karvo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Alqiyama ba za ta tashi ba har sai rana ta vullo daga mafaxarta, idan ta vullo mutane suka ganta a sannan sai su yi imani gaba xaya to a wannan lokacin shi ne: (Rai imaninta ba zai yi mata amfani ba, idan dai ba ta riga ta yi imani ba kafin wannan lokacin” Sannan sai ya karanto wannan ayar data gabata.

An karvo daga Abu Musa, Abdullahi xan Qais, Al-Ash’ariy (R.A) daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Haqiqa Allah (S.W.T) yana shimfixa hannunsa da daddare domin ya karvi tuban bawan da yayi savo da rana sannan yana shimfixa hannunsa da rana domin ya karvi tuban bawan da yayi savo da daddare har sai rana ta vullo daga mafaxarta” [Muslim ya ruwaito shi].

An karvo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Ma’aikin Allah (ﷺ) ya ce: “Dukkan wanda ya tuba kafin rana ta vullo ta mafaxarta to Allah zai karvi tubansa” [Muslim ya ruwaito shi].

Haka kuma Allah ba ya karvar tuban bawa yayin da ya kai lokacin gargara kamar yadda ya zo a cikin hadisin Abdullahi xan Umar (R.A) daga Annabi (ﷺ) cewa: “Haqiqa Allah yana karvar tuban bawa matuqar bai kai lokacin gargara ba”. Imam Attirmizi ya ce: “Wannan hadisin Hasan ne".

Kuma ma’anarsa idan dai har rai bai kai ga maqogwaro ba. Ma’ana idan dai mutuwa bata halarto shi ba. Domin ba a la’akari da tuba idan mutuwa ta halarto. Saboda faxin Allah (S.W.T) cewa:

( وَلَيْسَتِ التَّوْبَةُ لِلَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ حَتَّى إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ الْمَوْتُ قَالَ إِنِّي تُبْتُ الْآَنَ وَلَا الَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمْ كُفَّارٌ أُولَئِكَ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا 18 ) [النساء: 18]

(Ita tuba ba ta kasance abar karva ga waxannan da suka yi mummunan aiki alhalin basu tuba ba tuntuni, har sai da mutuwa ta halarto ma xaya daga cikinsu, sai ka ji shi yana cewa, “Ni na tuba a yanzu”. Da kuma waxannan da suke mutuwa alhalin suna kafirai).

Ya ku bayin Allah! Haqiqa tuba zuwa ga Allah tana tabbatarwa da bawa samun arziki na har abada, da kuma rayuwa mai daxi a nan duniya da kuma lahira. Allah maxaukakin sarki ya ce:

( مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَى وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ 97 ) [النحل: 97]

(Duk wanda ya aikata wani aiki na-gari, namiji ne ko mace, alhalin yana mumini to za mu rayar da shi rayuwa mai daxi, sannan kuma za mu saka masu da ladansu, ma fi kyau daga abin da suka kasance suna aikatawa).

Sakamakon tuban muminai ga Ubangijinsu hakan yana sawa su sami zaman lafiya, da shiriyar Allah maxaukakin sarki ya ce:

( الَّذِينَ آَمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ 82 ) [الأنعام: 82]

(Waxannan da suka yi imani, kuma ba su jirkita imaninsu ba da zalunci to irin waxannan suna da amintuwa, kuma su ne shiryayyu).

Ma’ana: Waxanda suka gaskata Ubangiji da Manzonsa suka yi aiki da shari’arsa, kuma basu cakuxa imaninsu ba da shirka, irin waxannan suke da nutsuwa da aminci, kuma su ne waxanda suka dace da bin tafarki na gaskiya, to idan tuba ya samu karvuwa, to aminci da shiriya sun samu.

Daga cikin amfanin tuba, akwai canza munanan aiyuka da kyawawa, da kuma shafe guraban munanan aiyuka. Kamar yadda ya zo a cikin faxin Ubangiji maxaukakin sarki:

( إِلَّا مَنْ تَابَ وَآَمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَحِيمًا 70 ) [الفرقان: 70]

“Sai dai fa wanda ya tuba, ya yi imani, ya kuma aikata aiki nagari, to irin waxannan su ne Allah yake canza munanan aiyukansu su zama kyawawa. Kuma Allah ya kasance mai gafara ne mai jin qai”.

Haqiqa Allah (S.W.T) ya bayyana qarara a cikin wannan ayar cewa, waxannan da suke yi zina da wanda aka ambata a tare da su, idan suka tuba, suka yi imani, suka aikata aiki nagar, to Allah zai canza munanan aiyukansu su zama kyawawa. Wannan yana nuna cewa, tuba daga aikata zina tana tafiyar da gurbinta. waxannan da suke cewa: Wanda duk ya yi zina da wata mace, wai ba ta halatta a gare shi ya aure ta ba, ko da sun tuba su biyun sun kyautata aikinsu, to wannan magana ta su ba daidai ce ba. Domin an samu daga wajen sahabbai cewa ya halatta ya auri matar da ya yi zina da ita matuqar sun tuba.

Yana daga cikin amfanin tuba, rabauta da samun yardar Allah, da kuma kubuta daga wuta, kamar yadda Allah (S.W.T) ya faxa:

( وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللَّهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ وَمَنْ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا اللَّهُ وَلَمْ يُصِرُّوا عَلَى مَا فَعَلُوا وَهُمْ يَعْلَمُونَ 135 ) [آل عمران: 135]

(Waxannan da idan sun aikata wata alfasha ko kuma suka zalunci kawunansu, sai su tuna Allah, su nemi gafarar zunubansu, waye ya ke gafarta zunubai idan ba Allah ba. Sannan ba su dogewa akan abin da suka aikata alhalin suna sane. To irin waxannan sakamakonsu wata gafara ce daga wajen Ubangijinsu, da kuma aljannatai wanda qoramu suke gudana a qarqashinsu, suna masu dauwama a ciki. Madallah da ladan masu aiki).

Ma’ana: Idan sun aikata wani zunubi sai su biyo bayansa da tuba, da neman gafarar Ubangijinsu.

Yaku bayin Allah! Imam Ahmad da Imamul Bukhari sun ruwaito wani hadisi daga Abu Huraira shi kuma daga Annabi (ﷺ) ya ce: Haqiqa wani mutum ya aikata wani zunubi sai ya ce, "Ya Ubangiji ni na aikata wani zunubi ka gafarta min". Sai Ubangiji ya ce, "Bawana ya aikata wani zunubi, sai ya san cewa shi yana da Ubangiji wanda yake yafe zunubi, kuma yake kamu da shi zunubin, to haqiqa na yafewa bawana". Sannan kuma ya aikata wani zunubin sannan ya ce, "Ya Ubangiji haqiqa na aikata zunubi ka yafe min". Sai Ubangiji mai girma da buwaya ya ce. "Bawana ya san cewa yana da Ubangiji, wanda yake yafe zunubi, kuma yake kamu da shi, to haqiqa na gafartawa bawana". Sannan dai kuma ya qara aikata wani zunubi, sai ya ce, "Ya Ubangji na aikata zunubi ka gafarta min". Sai Allah ya ce, "Bawana ya aikata zunubi sannan ya san cewa yana da Ubangiji yana gafarta zunubai, kuma yana iya kamu akansa”.