islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Dogaro Ga Allah


10309
Surantawa
Tawakkali ga Allah madaukakin sarki babban abin buqata ne daga bawa, kuma umarni ne daga Allah ga bayinsa muminai, ya umarce su da haka a cikin kowane yanayi . Sannan maanar tawakkali shine natsuwar zuciya wajen dogaro ga Allah don samun abubuwan amfani ko tunkude sharri. Da ace bawa zai yi haqiqanin dogaro ga Allah, da ya isar masa kuma ya azurta shi, kamar yadda yake azurta tsuntsu da sauran dabbobi.

Manufofin huxubar

Bayanin ma’anar Tawakkali, da kuma mahimmancinsa ga mutum musulmi.

Bayanin cewa, tawakkali wani vangare ne na imani.

Bayanin a kan cewa, riqo da sababai ba ya kore tawakkali.

Haxa zukatan bayi da Ubangijinsu, da bayani cewa, duk bayi masu buqatuwa ne zuwa ga Allah.

Jan-kunne a kan camfa wasu watanni ko kwanaki da wasu al’adu na jahiliyya waxanda suke rushe tawakkali.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ku ‘yan uwa! Lallai neman arziki buqata ce da Allah ya kimsa a cikin dukkan abubuwa masu rai, ba xan Adam kawai ba. Saboda haka, da zarar alfijir ya keto, za ka ga mutane suna shirye-shiryen tafiya wajen neman arziki, kama daga manoma, ‘yan kasuwa, masu sana’o’in hannu, ma’aikata, kowa za ka ga yana qoqari, yana fafutika wajen neman rufin asiri. Wahalar da hakan yake da shi, yakan sa xan Adam wani lokaci, ya bi karkatattun hanyoyi, don cin ma muradinsa. Sai dai, addinin musulunci, bai yarda da haka ba, bai yarda musulmi ya fake da ojoro da algus, ko wulaqanta kai, ko zalunci, don ya samu abin da yake buqata na tarkacen wannan duniya mai qarewa ba. To idan haka ne, ina mafita? Ina maganin wannan bala’i na neman tara dukiya, ko ta wane hali da aka jarrabi wasu daga cikin mutanen da suke rayuwa kan wannan qwallon duniya tamu: Suna zaluntar junansu? Lallai mu sani- ya bayin Allah - mafita tana cikin dogaro ga Allah, mai arzutawa, mai bayarwa, wanda idan ya bayar, ba wanda ya isa ya hana, idan kuma ya hana, ba wanda ya isa ya bayar.

Wannan aqida ta dogaro ga Allah, ita ce Manzon Allah (ﷺ) ya cusa a cikin zukatan sahabbansa, kamar yadda yake cewa, “Da za ku dogara ga Allah, gaskiyar dogaro da shi, da ya arzuta ku, kamar yadda yake arzuta tsuntsaye. Su fita da safe, cikinsu wayam, su dawo da yamma, cikinsu ya cika dam.” Hadisi ne ingantacce, Tirmizi da Ibn Majah ne suka ruwaito shi.

Allah akbar! Dogaro ga Allah, shi ne kaxai ita ce mafita wajen samun yardar Allah. A neman arziki, mutum ya fita nema tare da cikakkiyar dogara ga Allah.

Ya ‘yan uwa! Ku duba ku ga yadda tsuntsaye suke yi: Su fita, alhali cikinsu wayam, amma su dawo cikinsu damdam, saboda tsabar dogaro ga Allah.

Ya ku ‘yan uwa! Lallai dogaro ga Allah, abu ne mai girma, kuma Allah ya umarci bayi baki xaya, da su dogara da shi, ko a wane irin yanayi suke. Allah yana cewa,

(وَلِلَّهِ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَإِلَيْهِ يُرْجَعُ الْأَمْرُ كُلُّهُ فَاعْبُدْهُ وَتَوَكَّلْ عَلَيْهِ وَمَا رَبُّكَ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ123) [هود: 123]

(Abin da ya vuya a sama da qasa na Allah ne, kuma gare shi ake mayar da al’amari baki xaya, don haka ka bauta masa shi kaxai, kuma ka dogara da shi. Allah ba mai gafala ba ne game da abin da kuke aikatawa).

Kuma Allah yana ce wa Manzonsa (ﷺ),

وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ وَكِيلًا3) [الأحزاب: 3]) (Ka dogara ga Allah. Allah ya isa abin dogaro a kai).

Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Wasu mutane za su shiga aljanna, zukatansu kamar zukatan tsuntsaye.”

Wato masu dogaro ga Allah, ko kuma sanyin rai.

Ya ku ‘yan uwa! Dogaro ga Allah iri biyu ne:

Na farko, dogaro ga Allah wajen samun buqatun rayuwa, da abin duniya, ko ije wata musiba ko larura.

Na biyu, dogaro ga Allah wajen sanin abin da Allah yake qauna, kuma ya yarda da shi, na imani da yaqini da jihadi da da’awa da makamancin haka. Kuma tsakanin waxannan nau’i guda biyu, akwai fifiko da rata mai yawa. Duk sanda bawa ya dogara ga Allah, dogaro iri na biyu, to Allah zai isar wa bawa, dogaro irin na farko. Amma idan ya dogara na farko, ban da na biyu, to Allah zai isar masa, amma ba kamar irin na biyu ba. Don haka, tawakkalin da ya fi girma, shi ne dogaro ga Allah wajen neman shiriya, da tace tauhidi, da kaxaita biyayya ga Manzon Allah (ﷺ). Kuma wannan shi ne dogaro da Allah irin wanda Annabawan Allah suka yi.

Ya ‘yan uwa! Ya kamata mu sani, mutum ya daina bin matakin da Allah ya tsara don faruwa, ko kuma samun wani abu, ba ya cikin dogaro ga Allah. Kamar mutum ya zauna, ba tare da ya tashi, ya nemi arziki ba, ya ce ya dogara ga Allah, idan Allah ya qaddara zai zama mawadaci, zai zama, ko da kuwa bai wahala ba. Wannan rashin fahimtar abin da ake ce wa dogaro ga Allah ne, da tavewa, da asara. A nan, tilas ne mutum ya tashi, ya bi matakan da suka zama wajibi, don samun wani abu. Kamar yadda hadisi ya nuna, shi mai dogaro ga Allah, yana da sifa biyu: Ta farko, fafutikar neman abin da yake buqata; na biyu, dogaro ga Allah, da sakankancewa a kan cewa Allah ne kaxai mai bayarwa. Duk wanda ya rasa waxannan siffofi guda biyu, to bai dogara ga Allah ba, kuma ya yi asara babba. Lallai dogaro ga Allah, shi ne matattarar imani.

Ya ku ‘yan uwa! Lallai abin mamaki ne ga mutumin da ya san yana da buqata, ko da yaushe ga Allah, amma ya qi dogara da shi: Ya san ya matsu zuwa gare shi, amma ba ya neman taimakonsa; ya san komai yana hannunsa, amma ba ya nema daga gare shi; ya san cewa yana tsananin tausayin bayinsa, amma zuciyarsa ta qi nutsuwa da shi. Lallai bawa, ya kamata ka sa ni cewa, babu wani abu da za ka samu, sai ka wahala, kuma ka dogara ga Allah. Lallai duk wanda ya dogara ga Allah, ya ishe shi. Duk wanda ya nemi taimakonsa, ya xamfaru da shi, zai inganta masa addininsa da rayuwarsa. Duk wanda ya ruxu da kansa, zuciyarsa ta katse daga mahaliccinsa, ya tave, ya gama yawo. Sau tari za ka ga marar galihu mai rauni ya dogara ga Allah, Allah ya qarfafe shi. Hakanan sau tari za ka ga wanda yake ji da qarfi ya dogara ga qarfinsa. Amma qarfin bai tsinana masa komai ba yayin da yake cikin matsananciyar buqata. Babu sa'ada ga xan adam sai cikin bautar Allah ta'ala. Don haka shi ne gatansa shi ne mai taimakonsa.

Ya ku muminai, ku sani mumin ba shi da gata sai wajen Allah ta’ala, shi ne qarfinsa shi ne gatansa.

Allah yana cewa,

(إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ اللَّهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ وَإِذَا تُلِيَتْ عَلَيْهِمْ آَيَاتُهُ زَادَتْهُمْ إِيمَانًا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ2) [الأنفال: 2]

(Kaxai dai, masu imani, su ne waxanda idan aka ambaci Allah, zukatansu sukan ji tsoro, kuma idan aka karanta musu ayoyin, sai su qara musu ban-gaskiya, kuma ga Ubangijinsu shi kaxai, suke dogaro).

Allah ya amfane mu da abin da muka ji, ya ba mu damar aiki da shi. Alhamdu lillaahi rabbil aalamiin….

p>Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsa suka yi koyi da sunnarsa, har zuwa tashin qiyama. Bayan haka:

Ya ‘yan uwa! Lallai tilas a kan bawa, ya bi matakai, amma ba zai dogara da su ba, sai dai ya dogara ga Ubangijinsu. Manzon Allah (ﷺ) ya fi kowa dogaro ga Allah, amma yana bin duk wani mataki da ya zama wajibi. Bari ma, Allah ne yake umartarsa, shi da sahabbai, da yin haka, kamar yadda Allah yake cewa,

(يُجَادِلُونَكَ فِي الْحَقِّ بَعْدَمَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى الْمَوْتِ وَهُمْ يَنْظُرُونَ6) [الأنفال: 6]

(Ku yi tanadin abin da za ku iya, na qarfi da turkakkun dawaki, da za ku razana maqiyan Allah kuma maqiyanku da su).

Ya ku ‘yan uwa! Ya kamata ku sani, yana daga cikin abin da yake kore dogaro ga Allah, camfe-camfe, ko dai da ranaku da watanni, ko da dabbobi, ko tsuntsaye, ko kuma masu nakasa a jiki, kamar kutare, da tafiya wajen bokaye, da ‘yan tsibbu, da matsafa, da ‘yan duba, da makamantansu.

Ya ku ‘yan uwa! Ku sani, lallai dogaro ga Allah shi kaxai, da fawwala al’amura zuwa gare shi, shi kaxai, da qudurta cewa shi kaxai ne yake amfanarwa ko cutarwa, da nesantar duk wani camfi, abubuwa ne da suka zama wajibi mutum ya qudurce a cikin zuciyarsa. Kamar yadda Allah ya ce,

(وَإِنْ يَمْسَسْكَ اللَّهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إِلَّا هُوَ وَإِنْ يُرِدْكَ بِخَيْرٍ فَلَا رَادَّ لِفَضْلِهِ يُصِيبُ بِهِ مَنْ يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَهُوَ الْغَفُورُ107) [يونس: 107 (Idan Allah ya shafe ka da wata cuta, babu mai yaye ta, sai shi, idan kuma ya shafe ka da wani alheri, babu mai iya ture falalarsa. Yana samun wanda ya so daga cikin bayinsa da ita, kuma shi mai gafara ne, mai jin qai).

Kuma Allah ya ce,

(قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ65) [النمل: ٦٥ ].

(Ka ce, “Ba wanda ya san gaibu cikin sama da qasa, sai Allah).

Ya ‘yan uwana a cikin addinin musulunci! Haqiqa Allah ya xaukaka wannan al’umma, kuma ya tsabtace ta daga dukkan dattin jahiliyya. Mu sani, ‘yan uwa, yana cikin raunin imani, da rashin dogaro ga Allah, abin da muke gani mutane suna aikatawa a yau. Ka ga wani ya gina rayuwarsa gabaxaya a kan taurari da watanni: Idan tauraro kaza ya zo, akwai sa’a a ciki; idan wata kaza ya zo, ba sa’a a ciki. Kai ma, har ma a wata kaza, ba a yin aure ko tafiya. Lallai wannan yana daga cikin shirka. Allah ya kiyaye mu. Irin waxannan mutane, sai ka rasa da wane addini suka yi imani. Kai sai ka ce, ina ma tunaninsu yake? Wane irin tunani suka yi? Waxannan abubuwa da suke camfawa, su kansu ba za su iya amfanar da kansu ba, ko cutarwa, ballantana su amfanar da wani. Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya faxa a cikin hadisi, “Cuta ba ta yaxuwa da kanta, ba camfi, ba qwanqwami, ba camfi da watan Safar.”

Ya ‘yan uwa! Irin wannan faxakarwa da ake yi, ba ana yi don komai ba ne, sai don nasiha ga bayin Allah, sai don yaxuwar da waxannan abubuwa suka yi a cikin al’umma, kuma sai don kada masu raunin imani su faxa cikin waxannan qazaman aqidu, da ruvavvun al’adu. Kuma tilas ne malamai da xalibai, su tsaya tsaye wajen tsamo mutane daga cikin irin wannan ruxu, da rashin nutsuwa na camfi, zuwa ga kwanciyar hankali da nutsuwa ta addini da ingantacciyar aqida. Allah yana cewa,

(وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ مَنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ قُلْ أَفَرَأَيْتُمْ مَا تَدْعُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ إِنْ أَرَادَنِيَ اللَّهُ بِضُرٍّ هَلْ هُنَّ كَاشِفَاتُ ضُرِّهِ أَوْ أَرَادَنِي بِرَحْمَةٍ هَلْ هُنَّ مُمْسِكَاتُ رَحْمَتِهِ قُلْ حَسْبِيَ اللَّهُ عَلَيْهِ يَتَوَكَّلُ الْمُتَوَكِّلُونَ38) [الزمر: 38]

(Ka ce, “Ku ba ni labari kan abin da kuke kira, koma-bayan Allah. Idan Allah ya nufe ni da wata cuta, shin su za su yaye cutarsa, ko kuwa idan ya nufe ni da jin qai, shin za su riqe rahamarsa?” Ka ce, “Allah ya wadace ni, gare shi ne masu dogaro suke dogara).