Imani Da Qaddara


8849
Surantawa
Babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da qaddarar Allah. Wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne, kuma abinda be so faruwar sa ba, to haqiqa bazai faru ba. Haka kuma lallai aluma da zata taru gaba daya domin ta cutar da bawa da wani abu, to ba zasu iya ba saidai da abinda Allah ya rubuta zai same shi. Hakanan da zasu hadu domin su amfanar dashi, ba zasu iya ba face da abinda Allah ya rubuta.

Manufofin huxubar

Bayani a kan ma’anar imani da qaddara. Da kasancewarsa rukuni ne na imani.

Bayani a kan cewa, qaddara ba hujja ba ce wajen savon Allah.

Bayani abin da ya wajaba a kan bawa idan qaddara ta same shi.

Gargaxi a kan waxxanda suka vace game da sha’anin qaddara.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka, ya ‘yan uwa! Maganarmu a yau ta shafi xaya daga cikin rukunan imani guda shida, wanda duk wanda bai yi imani da shi ba, ko kuma ya yi musu a kansa, to Allah ba zai karvi ayyukansa ko qanana, ko manya ba. Shi ne bayar da gaskiya da qaddara. Rukuni ne mai girma, wanda ta hanyarsa mutum yake samun nutsuwa a rayuwarsa, ya kuma sami amsoshi game da abubuwa da yawa, da suka shige masa duhu. Allah yana cewa,

(إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَر49)ٍ [القمر: 49]

(Mun halicci komai da qaddara). Kuma Allah yana cewa,

(الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّى2 وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَى3) [الأعلى: ٢ – ٣].

(Shi ne wanda ya yi halitta, kuma ya daidaita ta, kuma shi ne wanda ya qaddara abubuwa, kuma ya shiryar da su).

Kuma Allah yana cewa,

(وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ فَقَدَّرَهُ تَقْدِيرًا2) [الفرقان: 2]

“Kuma ya halicci kowane abu, kuma ya qaddara shi, qaddarawa.”

Ayoyi da suke tabbatar da wannan rukuni, sun fi a qirga, kuma a cikin sunnar Manzon Allah (ﷺ) ma wuri daban-daban, ya tabbatar da wannan rukuni mai girma. Misali, a cikin hadisin da mala’ika Jibrilu ya zo wajen Annabi (ﷺ), yana tambayar sa, da ya tambaye shi kan imani, sai ya ce, “Imani shi ne, ka bayar da gaskiya da Allah, da mala’ikunsa, da littattafansa, da Manzanninsa, da ranar qarshe, da yarda da qaddara, mai daxi da mara daxi.” Sai Jibrilu ya ce, “Ka yi gaskiya!” Muslim ne ya ruwaito.

Ya ku ‘yan uwa! Abin da ake nufi da qaddara, shi ne ilimin Allah Ta’ala, wanda ya rigaya tun fil-azal, da abubuwa kafin su auku, kuma Allah ya rubuta su daki-daki, kafin ya halicci sama da qasa, da shekara dubu hamsin, kuma babu abin da zai auku, face da ganin damarsa, kuma shi ya halicce shi. Wannan shi ne bayar da gaskiya da qaddara wajen sahabbai, kuma shi ne bayar da gaskiya a wajen ahlussunnah. Don haka, tilas ne ga duk wani musulmi, ya yarda cewa babu wani abu da zai faru cikin mulkin Allah, wanda sai daga baya Allah zai san shi. A’a, Allah ya rigaya, ya san komai, tun fil-azal, kuma ya rubuta shi a allon qaddara (lauhil mahfuuz), kamar yadda ya zo a hadisin, kuma kamar yadda Allah yake cewa,

(إِنَّ ذَلِكَ فِي كِتَابٍ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ70) [الحج: 70]

“Lallai hakan, yana cikin littafi, lallai hakan mai sauqi ne wurin Allah.”

Don haka, babu wani abu da zai auku, face sai Allah ya ga dama, kuma idan zai auku, zai auku ne, kamar yadda Allah ya zartar. Allah yana cewa,

(وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا30 يُدْخِلُ مَنْ يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا31) [الإنسان: ٣٠ - ٣١].

(Ba kwa nufin aikata wani abu, sai Allah ya yi nufi. Lallai Allah masani ne, mai azanci, yana shigar da wanda ya yi nufi cikin rahamarsa).

Ya xan uwa! Ka sani, babu tilas ga xan Adam kan ayyukansa, a aqida ta musulunci. Mutum yana da dama, da kuma zavi, na ya aikata abin da ya ga dama, kamar yadda yake cewa,

(وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ10) [البلد: ١٠].

(Kuma mun shiryar da shi hanyoyi biyu).

Wato na alheri, da na sharri. Don haka, shi xan Adam, shi ne yake zavar abin da ya ga dama, kuma sanin Allah, ba ya nufin Allah ya yi masa tilas ba ne. Don ba daidai ba ne, mutum ya kafa hujja da qaddara wajen savon Allah, kamar yadda wasu mutane suke yi.

Ibni Taimiyya ya ce, «Wannan maganar banza ce. Wato mutum ya kafa hujja da qaddara a kan sava wa Allah, saboda imma dai qaddara ta zama hujja ga kowa da kowa, ko kuma ba hujja ba ce ga kowa da kowa. To idan qaddara hujja ce ga kowa da kowa, to babu wanda yake da dama ya yi musu ko inkari ga wanda ya cuce shi, ya zage shi, kuma ya qwace masa dukiyarsa, ya vata masa matansa, ya sare da takobi a wuya, kuma ya lalata masa gonarsa da ‘ya’yansa. domin ba zai cuce shi ba, sai da qaddara. Babu wanda zai yarda a cuce shi, a kafa masa hujja da qaddara. Abu na biyu, idan qaddara hujja ce, to da Iblis, da Fir’auna da mutane Annabi Nuhu da Adawa da sauran masu savon Allah, waxanda Allah ya halakar da su, da sun sami hujja. Haka kuwa abu ne da babu wani mai bin wani addini da zai yarda da shi. Abu na uku, da qaddara hujja ce, to da babu bambanci tsakanin bayin Allah na qwarai da fajirai. Wanda ya sava ga tunani na qwarai, ya kuma sava da faxin Allah cewa,

(وَمَا يَسْتَوِي الْأَعْمَى وَالْبَصِيرُ19 وَلَا الظُّلُمَاتُ وَلَا النُّورُ20 وَلَا الظِّلُّ وَلَا الْحَرُورُ21 وَمَا يَسْتَوِي الْأَحْيَاءُ وَلَا الْأَمْوَاتُ22) [فاطر: ١٩ – ٢٢].

“Makaho ba zai daidaitu da mai gani ba, haka duhu ba zai yi daidai da haske ba, haka inuwa ba za ta yi daidai da zafi ba, haka matattu ba za su yi daidai da masu rai ba.”

Kuma yana cewa,

(أَمْ نَجْعَلُ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَالْمُفْسِدِينَ فِي الْأَرْضِ أَمْ نَجْعَلُ الْمُتَّقِينَ كَالْفُجَّارِ28) [ص: 28]

(Ko za mu sanya waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na qwarai kamar masu varna a doron qasa, ko kuma za mu sanya masu taqawa su zama daidai da fajirai).

Abu na huxu: Ita qaddar imani aka ce mu yi da ita, ba kafa hujja ba. Duk wanda ya kafa hujja da qaddara to hujjarsa ta banza ce. Duk kuma wanda ya ba da hanzari da qaddara to hanzarinsa ba abin karva ba ne. Da ana karvar hujja da qaddara to da an karvi ta Iblis da sauran masu savo. Da qaddara hujja ce ga bayi da babu wani da za a yi masa azaba a nan duniya ko a lahira. Da ana hujja da qaddara da ba yanke hannun varawo ba, ba a kashe wanda ya yi kisan kai ba, da ba wanda za a yi wa haddi don ya yi wani laifi. Kai da ma ba wanda za a yaqa, ko a yi umarni da wani abu na shari’a ko hana wani mummunan abu.

Abu na biyar, an tambayi Manzon Allah (ﷺ), “Idan dai Allah ya rubuta komai, to meye amfanin aikin da bayi za su yi?” Sai ya ce, “A’a! Ku yi aiki. Kowa abin horewa ne ga abin da aka halicce shi don shi.” Abu na shida, idan dai rubutu da Allah ya yi, zai zamo hujja ga masu savo, to me ya sa ba zai zama hujja ba wajen ci da sha, da makamantan haka? Ai Allah ya qaddara masa ci da sha, da sauransu, amma ba zai qoshi ba, ko ya daina ci, sai ya ci, ya sha. Me ya sa ba zai ce, tunda Allah ya rubuta, ba sai na ci, ko na sha ba, idan na zauna haka ma, qaddara za ta biyamin buqatata? Ko kuwa haihuwa: Ai ita ma qaddara ce, me ya sa mutum ba ya zama, ya qi yin aure, ya ce, idan dai Allah ya rubuta mini xa, zan same shi, ko ban kusanci mace ba. Babu mai faxin haka, sai wawa. To haka ma abin da yake wajen bin Allah, ko sava masa.

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kuma tsira da aminci su tabbata ga mafi xaukakar Annabawa da Manzanni, Annabinmu, Muhammad, da iyalensa da sahabbansa gabaxaya. Bayan haka:

Akwai matakan qaddara guda huxu:

Mataki na farko: Allah ya san komai, samamme da ma wanda ba samamme ba. Ya san abin a faru da abin yake faruwa, da wanda zai faru nan gaba idan zai faru ya ya zai faru. Hujja a kan wannan shi ne faxin Allah:

(لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ وَأَنَّ اللَّهَ قَدْ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيْءٍ عِلْمًا12) [الطلاق: 12]

(Don ku san cewa, lalle Allah mai iko ne a kan dukkan komai, kuma iliminsa ya kewaye komai).

Mataki na biyu: Allah ya rubuta komai da zai faru har zuwa tashin qiyama. Allah yana cewa:

(أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ إِنَّ ذَلِكَ فِي كِتَابٍ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ70) [الحج: 70]

(Shin ba ka sani ba ne, cewa Allah yana sane da abin da yake cikin sama da qasa. Lalle wannan yana cikin littafi. Lalle wannan wani abu ne mai sauki a gurin Allah).

Yana cewa,

(وَكُلَّ شَيْءٍ أحْصَيْنَاهُ فِي إِمَامٍ مُبِينٍ12) [يس: 12]

(Kowane abu mun lissfe shi a cikin wani littafi mai bayyanawa).

Ya zo a sunna cikin hadisin Abdullah xan Amr bn Ass, Manzo Allah ya ce, (Allah ya rubuta abubuwan day a qaddarawa halitta kafin ya halitta sammai da qasa da shekara dubu hamsin.

Mataki na uku: Sai Allah ya so faruwar abu, domin duk abin da Allah ya so wakanarsa zai wakana, abin da bai ga damar wakanarsa ba zai wakana ba. Allah yana cewa,

(إِنَّمَا أَمْرُهُ إِذَا أَرَادَ شَيْئًا أَنْ يَقُولَ لَهُ كُنْ فَيَكُونُ82) [يس: 82]

(Kawai al’amarinsa, idan ya yi nufin wani abu sai ya ce da shi, kasance, sai ya kasance).

Kuma Allah yana cewa:

(وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ29) [التكوير: 29]

(Kuma ba abin da kuka so ne yake kasancewa ba, sai abin da Allah Ubangijin talikai ya so wakanarsa).

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abu Hurairah (R.A.) y ace, Manzon Allah (ﷺ) y ace, "Ka da xayanku ya ce, Ya Allah ka gafarta mani in ka ga dama. Ya Allah ka ji qaina in ka ga dama. Ya sa gaske cikin addu'arsa, domin shi Allah yana aikata abin da ya ga dama ne, babu mai tilasta shi).

Mataki na huxu: Halittar Allah ga abubuwa da samara da su da qudurarsa cikakkiya. Allah shi ne ya halicci kowane mai aiki da aikinsa, da duk mai motsi da motsinsa, dad k mai sukuni da sukuninsa. Allah ta'ala ya ce:

(خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ فَاعْبُدُوهُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ102) [الأنعام: 102]

Ma’ana: (Allah ne mahallicin komai, kuma shi wakili ne ga dukkan komai).

Kuma Allah yana cewa,

(وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ96) [الصافات: 96]

(Kuma Allah ne ya halicce ku da abin da suka kasance suna aikaitawa).

Bukhari ya ruwaito daga Imaran bn Husaini, daga Annabi (ﷺ) ya ce: "Allah yana nan, lokacin da babu wani abu tare da shi. Kuma al'arshinsa ya kasance a kan ruwa. Kuma ya rubuta komai acikn lauhul mahfuz. Kuma ya halicci sammai da qasa).

Don haka dole ne musulmi ya yi imani da waxannan matakai na qaddara guda huxu. Duk wanda ya musunta xaya daga cikinsu to bai yi imani da qaddara ba.

Ya ku bayin Allah! Ku sani cewa, Imani da qaddara yana fa'idoji, waxanda su ne kamar haka:

Dogaro ga Allah, lokacin da bawa ya bi matakan da ya kamata ya bi. Domin Allah shi ne wanda yake halittar sababi, da abin da sababin yake haifarwa.

Samun nutsuwar zuciya. Saboda bawa ya san cewa, duk abin ya faru qaddara ce daga Ubangiji.

Rashin jiji-da-kai lokacin da bawa zai samu muradinsa. Domin haka qaddara ce daga Allah, domin shi ne ya hore masa hanyoyin samin alheri. Don haka sai ya godewa Allah, ya gujewa jiji-da-kai.

Rabuwa da damuwa da vacin rai lokacin da bawa ya rasa samun abin da ya yi muradi. Domin hakan ya faru ne da qaddarar Allah da hukuncinsa. Don haka sai ya yi haquri Allah ya ba shi lada a kan hakan.

Ya ‘yan uwa! Haqiqa Allah yana cewa,

(مَا أَصَابَ مِنْ مُصِيبَةٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ وَمَنْ يُؤْمِنْ بِاللَّهِ يَهْدِ قَلْبَهُ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ11) [التغابن: 11]

.

(Babu wata masifa da za ta faru, sai da izinin Allah. Duk wanda ya bayar da gaskiya da Allah, to Allah zai shiryar da zuciyarsa. Allah masani ne da komai.)Allah yana cewa,

(مَا أَصَابَ مِنْ مُصِيبَةٍ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي أَنْفُسِكُمْ إِلَّا فِي كِتَابٍ مِنْ قَبْلِ أَنْ نَبْرَأَهَا إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ22) [الحديد: 22]

(Babu wata masifa da za ta faru, face sai tana cikin littafi, tun gabanin mu halicce ta. Lallai hakan, mai sauqi ne a wajen Allah).

Kuma Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Ya kai xan Adam! Ka sani, da al’umma baki xaya za su taru, don su cuce ka da wani abu, to ba za su iya ba, sai da abin da Allah ya rubuta maka. Haka ma, da za su taru don su amfane ka da wani abu, ba za su iya mafanarka ba, sai da abin da Allah ya rubuta.” Kuma Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, “Idan wani abu ya same ka, kada ka ce ina ma na yi kaza, ko kaza, a’a, ka ce, qaddara ce ta Allah, kuma abin da ya ga dama, ya aikata. Domin ‘da’ tana buxe qofar shaixan.” Haka kuma, ya tabbata a cikin hadisi, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Abin mamaki ga lamarin mumini: Idan abin daxi ya same shi, sai ya gode wa Allah, hakan sai ya zamo masa alheri; idan cuta ta same shi, sai ya yi haquri, hakan sai ya zame masa alheri.” Ali ya rawaito cewa, Manzon Allah (ﷺ) wata rana ya ke wajen jana’iza, sai ya xauki wani abu, yana tona qasa da shi. Sai ya ce, “Babu wani mutum, face an rubuta mazauninsa na wuta ko aljanna.” Sai suka ce, “Ya Ma’aikin Allah! Ba ma dogara da abin da aka rubuta mana ba, mu daina aiki?” Sai ya ce, “A’a! Ku yi aiki. Kowa za a sauqaqe shi ga abin da aka halicce shi don shi. Wanda ya zamo mai rabo, sai a sawwaqe shi ga aikin masu rabi, haka wanda yake cikin tavvavu, sai a sawwaqe masa aikin tavavvu.”

Ku sani, ya ‘yan uwa! Qungiyoyi biyu ne suka vata a babin qaddara: Qadariyya, waxanda suka ce abubuwa na faruwa ne ba tare da sanin Allah ba, da Jabariyya, waxanda suka ce xan Adam tilas ake yi masa kan abin da yake aikatawa. Dukkaninsu vatattu ne. Allah ya qaddara komai da komai, ya kuma bai wa xan Adam iko na ya zavi abin da ya ga dama. Kamar yadda Allah ya ce, “Lallai mun shiryar da xan Adam tafarki, ko dai ya zama mai godiya, ko ya zama mai butulci.” Yahaya bin Ya’amur ya ce, farkon wanda ya fara magana kan qaddara a Basrah, shi ne Ma’abad Aljuhani. Ya ce, “Sai muka yunqura, ni da Humaid bin Abdurrahman, muka tafi hajji ko umarah, sai muka ce, ina ma mu haxu da wani cikin sahabbai, mu tambaye shi kan abin da su Ma’abad suke faxi kan qaddara. Sai muka yi katari da Abdullahi xan Umar, zai shiga masallaci. Sai muka tare shi, ni da abokina, xaya yana damansa, xaya yana hagunsa. Sai na fahimci abokina zai bar ni, na yi magana. Sai na ce, “Abu Abdurrahman, wasu mutane sun bayyana a wajenmu, suna karatun Alqur’ani, suna bibiyar ilimi.” Ya faxi labarinsu, kuma ya ce, “Kuma suna cewa, sai abu ya faru, sannan Allah yake sani. Suka ce babu qaddara.” Sai ya ce, “Idan ka haxu da su, ka gaya musu cewa, bari ba su suma ba su sani. Na rantse da wanda Abdullahi bin Umar yake rantsuwa da shi, da xayansu zai ciyar da misalin dutsen Uhud na zinare, Allah ba zai karva ba, har sai ya ba da gaskiya da qaddara.” Sannan ya karanto dogon hadisin nan na zuwan Jibirilu, da tambayoyi da ya yi wan Manzon Allah (ﷺ).

Tags: