Muhimmancin umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummuna


4989
Surantawa
Umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna aiki ne babba, da yawan muttane sun gafala daga barin shi. Lallai ba karamar annoba bace wadda karshenta ba zaiyi kyau ba ga daidaikun mutane da aluma gaba-daya, yayin da daliban ilimi da shiryayyun matasa zasuyi ko-in-kula da kutsawa cikin fagagen gyara na rayuwar yau da gobe, don umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna.

Manufofin huxubar

Bayyana ma’anar Umarni da kyakkyawan aiki da hani ga Mummuna.

Tsoratarwa daga Baqin halaye munana.

bayanin matakan hana mummunan aiki.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Yaku ‘yan uwa musulmi : Canza mummunan aiki yana da matakai waxanda Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana su a cikin hadisin da Imam Muslim ya rawaito daga Abu Sa’id Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi –, ya ce, na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Duk wanda ya ga mummuna abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, idan ba zai iya ba, to da zuciyarsa (wato ya qi abun) wannan shi ne mafi raunin imani”.

Hakanan Manzon Allah (S.A.W) ya qara fito da waxannan matakai a fili a cikin hadisin Abdullahi xan Mas’ud – Allah ya yarda shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Babu wani Annabi da Allah ya aiko shi gabanina face yana da tatattun mabiya daga cikin al’ummarsa, da sahabbai da suke riqo da sunnarshi, suna koyi da umarninsa, sannan sai wasu su biyo bayansu, suna faxin abin da ba sa aikata wa, suna aikata abin da ba a umarce su ba, duk wanda ya yi jihadi a kansu da hannunsa to wannan mumini ne, wanda ya yi jihadi a kansu da harshensa wannan ma mumini ne, wanda ya yi jihadi a kansu da zuciyarsa shi ma mumini ne. Amma bayan wannan to babu wani imani ko da daidai da qwayar zarra” (muslim ne ya rawaito).

Babban Malamin nan Ibnu – Qayyim yana cewa : “Haqiqa Annabi (S.A.W) ya shar’anta wa al’ummarsa wajabcin hana mummunan aiki, saboda a samu abin da Allah da Manzonsa suke so, amma idan hana mummnan aiki zai kawo samuwar abin da ya fi shi muni, yafi shi zama abin qi a wajen Allah da Manzonsa to ba ya dacewa a hana wannan mummunan aikin, duk da cewa Allah ba ya son wannan aiki, kuma ba ya son masu yin sa. Misalin irin wannan kuwa kamar inkari ga masu mulki ta hanyar fito – na – fito da tawaye gare su, saboda hakan shi ne asalin duk wata fitina da sharri. Sahabbai sun nemi izinin Manzon Allah (S.A.W) wajen yaqar shugabannin da suke jinkirta sallah ga barin lokacinta, suka ce “Ba ma yaqe su ba?” Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “A’a matuqar dai suna yin sallah” sannan ya ce, “Duk wanda ya ga wani abin qi daga shugabansa to ya yi haquri, kada ya cire hannunsa daga yi masa xa’a”.

Ya ci gaba da cewa : “Duk wanda ya lura da abin da ya gudana na manya da qananan fititntinu a cikin musulunci zai ga barin wannan asali (na bin shugabanni) shi ne asalinta, da rashin haquri a kan wani mummunan abu, sai aka nemi kawar da shi, sai hakan ya haifar da aikin da ya fi shi muni. Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana ganin abin qi a Makkah amma ba zai iya kawar da su, har ma lokacin da Allah ya bashi damar buxe Makka da mayar da ita garin musulunci ya yi niyyar ya canza xakin ka’aba ya mayar da shi akan ginin Annabi Ibrahim, amma tsoron abin da zai faru wanda ya fi wannan girma ya hana shi yin hakan, duk da yana da ikon yi xin, saboda zai yiwu Quraishawa ba za su iya xaukar hakan ba, saboda sababbin shiga musulunci ne, wannan ya sa ma Manzon Allah (S.A.W) bai yi umarni da amfani da hannu wajen inkari ga shugabanni ba, saboda abin da zai iya faruwa wanda ya fi abin da suke kai muni. Hana mummunan aiki yana da matakan huxu :

Kodai mummunan aikin ya gushe, kishiyarsa (aikin alheri) ya maye gurbinsa.

ko kuma mummunan aikin ya yi qaranci, koda bai gushe gaba xaya ba.

ko kuma ya gushe gaba xaya, wani mummunan abu irinsa ya maye gurbinsa.

ko kuma wanda yafi shi sharri da muni ya maye gurbinsa.

To a mataki na xaya da na biyu an shar’anta (a kawar da mummunan aiki a cikinsu), na uku kuwa sai a duba a ga abin da ya dace, amma mataki na huxu haramun ne a (kawar da mummunan aiki a wannan yanayi). (Duba littafin I’ilamul Muwaqqien).

‘Yan uwa musulmi : Ku sani cewa mai umarni da aiki kyakkyawa sharaxi ne a samu waxannan sharuxxai a tare da shi:

Ya zama musulmi mai tsoron Allah.

Ya zama balagagge, domin umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummuna ba ya wajaba akan yaro qarami.

Ya zama mai adalci, kuma mai ilimi, musamman ma akan abin da zai umarta ko ya hana xin.

Ya zama zai iya yin umarnin da hanin, saboda iko wajen yin abu shi ne abin da yake kawo a xora wa mutum aiki.

Ku ji tsoron Allah bayin Allah, ku yi abin da ya wajabta muku shi na umarni da aiki mai kyau, da hana mummunan aiki, sai ku rabauta, ku nisanci kawar da kai daga barin wannan aiki mai girma, saboda kawar da kai ga barin wannan aikin yana jawo sharri da varna ga al’umma da qasa gaba xaya. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa :

(فَلَوْلَا كَانَ مِنَ الْقُرُونِ مِنْ قَبْلِكُمْ أُولُو بَقِيَّةٍ يَنْهَوْنَ عَنِ الْفَسَادِ فِي الْأَرْضِ إِلَّا قَلِيلًا مِمَّنْ أَنْجَيْنَا مِنْهُمْ وَاتَّبَعَ الَّذِينَ ظَلَمُوا مَا أُتْرِفُوا فِيهِ وَكَانُوا مُجْرِمِينَ116) [هود: 116]

Ma’ana : “Ba don waxanda suka rage a cikin qarnonin da suka gabata ba, suna hana varna a bayan qasa, sai dai qaxan daga cikin waxanda muka tseratar daga cikinsu, waxanda suka yi zalunci suka bi abin da aka jiyar da su na daxi suka zama masu laifi”. (Hud : 116).

Ina roqon Allah Ta’ala ya yi mana gafara, ya sanya mu cikin waxanda suke umarni da kyakkyawan aiki suke hana mummuna. Haqiqa Allah Mai iko ne akan komai.

Tags: