Tafarkin kira zuwa ga Allah


12446
Surantawa
Yana daga cikin fitattun bangarori a cikin rayuwar annabawa, bangaren kira zuwa ga Allah madaukakin sarki, kuma wannan kira yana da tafarkinsa wanda yake bayyananne da babu rudani a ciki. Daga ciki akwai: ilimin abinda mutum ke kira zuwa gare shi, da aiki da abinda yake kira zuwa gare shi, da kaddamar da abu mafi muhimmanci sannan me bi masa, da siffatuwa da dabiu kyawawa, hade da sanya hikima yayin kira zuwa ga Allah.

Manufofin huxubar

Tunatar da mutane qoqarin da Annabawa suka yi wajen isar da saqon Allah.

Zaburar da masu wa’azi wajen koyi da Annabawa cikin tsarin kira zuwa ga addinin Allah.

Bada himma wajen sabuntar da hanyoyin da’awa daidai da halin da ake ciki.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Yaku ‘yan uwana masu sauraro, huxubarmu a yau tana magana ne akan tsarin da Annabawa suka bi, wajen kira zuwa ga addinin Allah Subhanahu Wa ta’ala.

Haqiqa tsarin da Annabawa suka bi wajen kiran mutane zuwa addinin Allah, tsari ne da ya wajaba akan dukkan musulmi da musulma su lazimce shi, su bi shi wajen kiran mutane zuwa ga addinin Allah, saboda shi ne mafi alherin tsari da xan adam ya sani a tarihi.

Haqiqanin kiran Annabawa shi ne kiran mutane zuwa ga tsarkake ibada ga Allah, da barin shirka da shi a cikin magana ne ko aiki, Allah ya ce :

(وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِي كُلِّ أُمَّةٍ رَسُولًا أَنِ اُعْبُدُوا اللَّهَ وَاجْتَنِبُوا الطَّاغُوتَ36) [النحل: 36]

Ma’ana : “Haqiqa mun aiko wa kowace al’umma Manzo, a kan su bautawa Allah su nisanci Xagutu”. (Annahal : 36).

Sannan Allah Mai girma da buwaya ya bayyana tsarin da Annabawa suka bi wajen kiran mutane zuwa ga addini daki – daki a cikin Alqur’ani. Ya bayyana yadda suka bijirar da musulunci ga xaixaikun mutane da al’ummu da masu mulki, da qarfafa da masu rauni, da mawadata da talakawa, da sauransu.

Ya ambaci labaran Annabawa da mutanensu, ya faxi irin yadda Allah ya ba su nasara, su da mabiyansu, da kuma yadda ya ruguza waxanda suka ja da su, suka yi musu girman kai, xaixaikun mutane ne ko jama’a, irinsu Fir’auna, da lamarudu, da irinsu Qaruna, Kai! Har ma da jama’u da qabilu, irinsu Adawa da Samudawa da sauransu.

Alqur’ani littafi ne da ya qunshi komai da komai, litatfi ne na tauhidi da imani, haka kuma littafi ne na ilimi da hikima da shari’a , littafi ne na addu’a da ibada, littafi ne na Umarni da kira, kamar yadda yake littafi ne na ambato.

Idan muka xauki Annabi Nuhu zamu ga salon da ya bi wajen yi wa mutanensa wa’azi, salo na hikima da haquri, da jan – hankali, Allah ya ce,

(لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرُهُ إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ59 قَالَ الْمَلَأُ مِنْ قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي ضَلَالٍ مُبِينٍ60 قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي ضَلَالَةٌ وَلَكِنِّي رَسُولٌ مِنْ رَبِّ الْعَالَمِينَ61 أُبَلِّغُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَأَنْصَحُ لَكُمْ وَأَعْلَمُ مِنَ اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ62 أَوَعَجِبْتُمْ أَنْ جَاءَكُمْ ذِكْرٌ مِنْ رَبِّكُمْ عَلَى رَجُلٍ مِنْكُمْ لِيُنْذِرَكُمْ وَلِتَتَّقُوا وَلَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ 63 فَكَذَّبُوهُ فَأَنْجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ فِي الْفُلْكِ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآَيَاتِنَا إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا عَمِينَ64) [الأعراف: ٥٩ - ٦٤].

Ma’ana : “Haqiqa mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, ya ce musu yaku mutane na ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa wanda ba shi ba, haqiqa ina ji muku tsoron azabar wani yini mai girma. Sai manyan gari daga cikin mutanensa suka ce, haqiqa mu muna ganin kana cikin vata mabayyani, sai ya ce musu, ya mutanena babu wani vata a tare da ni, Kaxai ni dai Manzone daga Ubangijin Talikai. Ina isar muku da saqonnin ubanjina ne, kuma ina muku nasiha, sannan na san wani abu dangane da Allah wanda ba ku sani ba. Yanzu kuna mamaki don tunatarwa ta zo muku daga wani mutum daga cikinku, don ya tunatar da ku, ko kwa ji tsoron Allah, kuma wala - alla a yi muku rahama. Sai suka qaryata shi, sai muka tseratar da shi da waxanda suka imani da shi a cikin jirgin ruwa, muka nutsar da waxanda suka qaryata da ayoyinmu, haqiqa sun kasance mutane ne makafi” (Al-a’araf : 59 – 63).

A waxannan ayoyi zamu ga yadda Annabi Nuhu yake yi wa mutanensa wa’azi, ta hanyar tausasawa da hikima – duk da irin munanan maganganun da suke faxa masa – . Ya fara musu wa’azi da kira zuwa ga tsarkake bauta ga Allah, sannan ya xora da tsoratar da su azabar Ubangiji idan suka kafirce suqa qi yin imani. To haka tsarin kiran dukkan Annabawa yake, wa’azi da tausasawa, da hikima, da haquri.

Fara wa’azi da tauhidi da barin shirka shi ne tsarin da dukkan Annabawa suka bi wajen da’awarsu, Allah Maxaukakin Sarki a cikin Alqur’ni ya hakaito mana cewa kowane Annabi abin da yake fara faxa wa mutanensa shi ne : “Ku bautawa Allah, ba ku da wani abin bautawa da gaskiya wanda ba shi ba”.

An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa Mu’azu xan Jabal - Allah ya yarda da shi – yayin da ya aika shi zuwa Yemen, “Haqiqa zaka isa wajen wasu mutane ma’abota littafi, idan ka isa wajensu ya zama abin da zaka fara kiransu gare shi, shi ne su shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Muhammad Manzon Allah ne, idan sun yi maka xa’a akan haka, sai ka sanar da su cewa Allah ya wajabta musu salloli biyar a kowane dare da yini, idan sun yi maka xa’a to ka faxa musu cewa Allah ya wajabta musu zakka, za a karva daga masu wadatarsu a mayar da ita ga talakawansu, idan sun yi maka xa’a akan haka, to ka kiyaye manya – manyan dukiyoyinsu, ka kuma ji tsoron addu’ar wanda aka zalunta, domin babu shamaki tsakaninta da Allah” Bukhari ne ya rawaito.

Yaku ‘yan uwana musulmi : Tausasawa a wajen wa’azi da faxin zance mai daxi ga wanda ake wa wa’azi wani abu ne da Allah ya yi umarni da shi, ya cewa Annabi Musa da Haruna yayin da za su je wajen Fir’auna :

(فَقُولَا لَهُ قَوْلًا لَيِّنًا لَعَلَّهُ يَتَذَكَّرُ أَوْ يَخْشَى44) [طه: 44]

Ma’ana : “Ku faxa masa magana mai taushi, wataqila ya wa’azantu ko ya ji tsoron Allah”. (Xaha :44 ). Haka ma amfani da hikima wajen wa’azi wani tsari ne da Allah ya girmama Annabawa da shi, mu lura da Annabi Yusuf (AS) (yadda ya yi amfani da hikima wajen kiran abokansa na kurkuku) ya ce musu :

(يَا صَاحِبَيِ السِّجْنِ أَأَرْبَابٌ مُتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ مَا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِهِ إِلَّا أَسْمَاءً سَمَّيْتُمُوهَا أَنْتُمْ وَآَبَاؤُكُمْ مَا أَنْزَلَ اللَّهُ بِهَا مِنْ سُلْطَانٍ إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ ذَلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ40) [يوسف: ٣٩ - ٤٠].

Ma’ana : “Ya ku abokaina na kurkuku, yanzu abin bautawa daban – daban su ne suka fi alheri ko kuwa Allah wanda yake shi xaya mai rinjaye. Ba komai kuke bauta wa ba, wanda ba Allah ba sai sunayen da kuka qirqire su, ku da iyayenku, wanda Allah bai saukar da wani dalili a kansu ba, hukunci gaba xaya na Allah ne, ya yi umarni kada a bautawa kowa sai shi kaxai, wannan shi ne addinin miqaqqe, amma ba fi yawan mutane ba su sani ba”. (Yusuf : 39 - 40).

(Haka lamarin yake idan muka duba labarin qissar Annabi Luxu da mutanensa, lokacin da yayi baqi, su kuma suka zo don yin lalata da waxannan baqi), sai Annabi Luxu ya ce da su – cikin hikima da tausasawa – :

)لَكُمْ فَاتَّقُوا اللَّهَ وَلَا تُخْزُونِ فِي ضَيْفِي أَلَيْسَ مِنْكُمْ رَجُلٌ رَشِيدٌ78) [هود: 78]

Ma’ana : “Ya mutanena ga ‘ya ‘yana mata nan, tsarkakakku ne gareku, ku ji tsoron Allah kada ku kunyata ni a cikin baqina, Yanzu babu wani shiryayye a cikinku”. (Hud : 78).

A wani wajen kwaxaitarwa da tsoratarwa nan ma Annabi Nuhu ya ce da mutanensa:

(فَقُلْتُ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ إِنَّهُ كَانَ غَفَّارًا10 يُرْسِلِ السَّمَاءَ عَلَيْكُمْ مِدْرَارًا11 وَيُمْدِدْكُمْ بِأَمْوَالٍ (وَبَنِينَ وَيَجْعَلْ لَكُمْ جَنَّاتٍ وَيَجْعَلْ لَكُمْ أَنْهَارًا 12 مَا لَكُمْ لَا تَرْجُونَ لِلَّهِ وَقَارًا 13وَقَدْ خَلَقَكُمْ أَطْوَارًا 14 [نوح: ١٠ - ١٤].

Ma’ana : “Na ce ku nemi gafarar ubangijinku haqiqa shi mai yawan gafara ne. zai qare ku da dukiya da ‘ya ‘ya, ya kuma sanya muku gonaki, ya sanya muku qoramu. Me ya same ku ba kwa neman nutsuwa a wurin Allah. Alhali ya halicceku mataki bayan mataki”. (Nuh : 10 – 14).

Yana cikin tsarin kiran Annabawa, yin wa’azin da duk lokacin da ya dace, da daddare ne ko da rana, (suna ribatar yanayin da ya dace). Allah Maxaukakin Sarki ya hakaito mana irin yadda Annabi Nuh ya yi amfani da dukkan lokutan da suka dace wajen kiran mutanensa zuwa ga Addinin Allah.

(قَالَ رَبِّ إِنِّي دَعَوْتُ قَوْمِي لَيْلًا وَنَهَارًا5) [نوح: 5]

Ma’ana : “”Nuhu ya ce, ya Ubangijina na kira mutanena dare da rana)

(Nuh : 5) Ya sake cewa:

(ثُمَّ إِنِّي أَعْلَنْتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارًا9) [نوح: 9]

“Sannan na bayyana musu (wa’azi) a bayyane, na yi musu (Wa’azi) a voye”. (Nuh : 9).

Hakanan Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana bin mutane a wurin aikin hajj a garin Makkah yana kiransu zuwa ga bauta wa Allah shi kaxai, ba tare da abokin tarayya ba.

‘Yan uwana musulmi wannan kaxan kenan daga cikin irin tsari da salo da Annabawa suke bi wajen wa’azi da ilmantarwa da kiran mutane zuwa ga addinin Allah. Zamu ga akwai ilimi da hikima da tausasawa da hankali a cikinsa, don haka wajibi ne a kanku ya ku masu kira zuwa ga Allah da masu tarbiyya ku yi koyi da su, don wa’azi ya yi amfani ya shiga cikin kunnuwa.

Allah ya yi mana Albarka cikin abin da muka ji, na Alqur’ani da Hadisi, Shi Allah Mai iko ne akan dukkan komai.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe ya tabbata ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su, har zuwa ranar sakamako gaba xaya. Bayan haka :

Yaku masu sauraro, yana cikin abin da tsarin kiran Annabawa ya bambanta da shi kawo dalilai gamsassu na hankali akan abin da suke kira a kai, Dalilan da duk mai hankali ba zai iya kawar da su ba, sai dai ya yi girman kai, ya qi gaskiya. Hakanan wajen kawo dalilan na shari’a, Idan muka duba qissar Annabi Ibrahim (A.S) zamu ga irin waxannan dalilai na hankali da ya yi amfani da su, wajen jawo hankalin mutanensa zuwa ga bautawa Allah shi kaxai, ba tare da shirka ba, Allah ya ce :

(وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لِأَبِيهِ آَزَرَ أَتَتَّخِذُ أَصْنَامًا آَلِهَةً إِنِّي أَرَاكَ وَقَوْمَكَ فِي ضَلَالٍ مُبِينٍ74 وَكَذَلِكَ نُرِي إِبْرَاهِيمَ مَلَكُوتَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلِيَكُونَ مِنَ الْمُوقِنِينَ75 فَلَمَّا جَنَّ عَلَيْهِ اللَّيْلُ رَأَى كَوْكَبًا قَالَ هَذَا رَبِّي فَلَمَّا أَفَلَ قَالَ لَا أُحِبُّ الْآَفِلِينَ76فَلَمَّا رَأَى الْقَمَرَ بَازِغًا قَالَ هَذَا رَبِّي فَلَمَّا أَفَلَ قَالَ لَئِنْ لَمْ يَهْدِنِي رَبِّي لَأَكُونَنَّ مِنَ الْقَوْمِ الضَّالِّينَ77فَلَمَّا رَأَى الشَّمْسَ بَازِغَةً قَالَ هَذَا رَبِّي هَذَا أَكْبَرُ فَلَمَّا أَفَلَتْ قَالَ يَا قَوْمِ إِنِّي بَرِيءٌ مِمَّا تُشْرِكُونَ78 إِنِّي وَجَّهْتُ وَجْهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ حَنِيفًا وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ79وَحَاجَّهُ قَوْمُهُ قَالَ أَتُحَاجُّونِّي فِي اللَّهِ وَقَدْ هَدَانِ وَلَا أَخَافُ مَا تُشْرِكُونَ بِهِ إِلَّا أَنْ يَشَاءَ رَبِّي شَيْئًا وَسِعَ رَبِّي كُلَّ شَيْءٍ عِلْمًا أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ80 وَكَيْفَ أَخَافُ مَا أَشْرَكْتُمْ وَلَا تَخَافُونَ أَنَّكُمْ أَشْرَكْتُمْ بِاللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ عَلَيْكُمْ سُلْطَانًا فَأَيُّ الْفَرِيقَيْنِ أَحَقُّ بِالْأَمْنِ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ81 الَّذِينَ آَمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ82وَتِلْكَ حُجَّتُنَا آَتَيْنَاهَا إِبْرَاهِيمَ عَلَى قَوْمِهِ نَرْفَعُ دَرَجَاتٍ مَنْ نَشَاءُ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٌ83 [الأنعام: ٧٤ – ٨٣]

Ma’ana : “Ka tuna yayin da Ibrahim ya ce wa babansa Azara, yanzu zaka riqi gumaka ababen bauta, lallai ni ina ganinka kai da mutanenka kuna cikin vata mabayyani. Hakanan muke nuna wa Ibrahim mulkin sammai da qassai don ya zama cikin masu yaqini. Yayin da dare ya yi, ya ga tauraro sai ya ce, “wannan ne Ubangijina” yayin da ya faxi (ya vace) sai (Annabi Ibrahim) ya ce bana son wanda yake faxu wa. Yayin da ya ga wata ya fito fili, sai ya ce wannan ne Ubangijina, yayin da ya vace, sai ya ce, in Ubangijina bai shirye ni ba zan kasance cikin mutane vatattu. Yayin da ya ga rana ta bayyana sai ya ce, wannan ne Ubangijina, wannan ma ya fi girma, yayin da ta faxi (ta vace), sai ya ce, ya mutanena ni na barranta daga abin da kuke shirka da shi. Na fuskantar da fuskata zuwa ga wanda ya halicci sammai da qassai, sannan ina mai karkata zuwa ga gaskiya, ba na cikin masu shirka. Sai mutanensa suka yi jayayya da shi, sai ya ce musu yanzu kuna jayayya da ni dangane da Allah, alhali ya shirye ni, ba na tsoron abin da kuke shirka da shi, sai dai abin da Allah ya so, Ubangijina ya yawalci komai da ilimi, ashe ba zaku wa’azantu ba. Kuma ta yaya zan ji tsoron abin da kuke shirka da shi, alhali ku ba kwa tsoron kun yi shirka da Allah a cikin abin da bai saukar muka da wani dalili a kansa ba. To wane jama’a ne (tsakanin ni da ku) ya fi cancanta da aminci in dai kun sani?. waxanda suka yi imani ba su haxa imaninsu da shirka ba, waxannan suna da cikakken aminci kuma su ne shiryayyu. Waxannan hujjojinmu ne muka baiwa Ibrahim a kan mutanensa, muna xaga darajar wanda muka so, haqiqa Ubangijinka mai hikima ne kuma masani”. (Al – An’am : 74 – 83).

A cikin waxanan ayoyi zamu ga hujjoji na hankali da Annabi Ibrahim ya buga wa mutanensa hujja da su, na bayyana cewa duk abin da baya amfanarwa ba ya cutarwa, ba ya dauwama, bai cancanta a bauta masa ba, Allah Maxaukakin Sarki Mahaliccin kowa da komai shi ne kaxai ya cancanta a bauta masa.

Idan mun duba qissar Annabi Musa da Fir’auna (zamu ga yadda Annabi Musa ya kafawa Fir’auna hujja ta hankali wadda ya gaza ture ta, yayin da Fir’auna ya tambayi Annabi Musa da Haruna ya ce, waye Ubangijinku, sai Annabi Musa ya ce masa ,

(قَالَ رَبُّنَا الَّذِي أَعْطَى كُلَّ شَيْءٍ خَلْقَهُ ثُمَّ هَدَى50) [طه: 50]

Ma’ana : “Ya ce Ubangijinmu shi ne wanda ya halicci dukkan komai kuma ya shiryar (da shi)”. (Xaha : 50). Irin waxannan misalai a qissar Annabi (S.A.W) suna da yawa.

Yaku Musulmi, ku nisanci savawa tsarin Annabawa wajen kira zuwa ga Allah, kada ku bi hanyoyin vatattu, irinsu khawajijawa, da ‘yan shi’a, da sauransu, wajen kira zuwa ga Allah.

Sannan wajibi akan masu wa’azi – malamai da xalibai – su amfanu da hanyoyin zamani da aka samu wajen kira zuwa ga addinin Allah, irinsu Internet, da kwamfuta, da salula da sauransu, ku duba ku ga yadda abokan gabarmu suka ribaci waxannan abubuwa don yaxa varnarsu.

Ku ji tsoron Allah – bayin Allah – Ku sani fiyayyar shiriya ita ce shiryar Manzon Allah (S.A.W), mu yi koyi da Manzon Allah wajen kiran mutane zuwa ga addini, mafi sharrin al’amura abubuwan da aka qaga, duk abin aka qaga kuwa bidi’a ce, dukkan bidi’a vata ce, dukkan vata kuwa yana cikin wuta.

Tags: