Hadarin mummunar shiga ga ya-mace musulma


6070
Surantawa
Allah madaukakin sarki yayi umarni acikin littafinsa me girma da katanguwar mata ,da lazimtar gidajensu,hakanan ya tsoratar dasu daga mummunar shiga da siranta magana ga mazace, domin kiyaye su daga fadawa cikin barna, da fadakar dasu daga sabubban barna. Lallai mummunar shigar mace, sharri ne me girman gaske gare ta da kuma alumma gaba daya,kuma babu abinda zai kiyaye mutuncin ya-mace face hijabin ta da kunyar ta.
Bayanin yadda za a magance wannan matsalar. Umartar mata musulmai da su kame kansu. Toshe qofofin fitina da suka yaxu a wannan zamani. Manufofin huxubar Huxuba Ta Farko Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Allah Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta. Bayan haka: Ya ku bayin Allah! Ku sani lallai yana daga cikin rahamar Allah ta’ala, da ya rufe wa bayinsa qofofin sharri, ya toshe duk wata qofa ta fitina, da savon Allah. Wanda duk ya buxe wannan qofa kuwa, to zai faxa cikin savon Allah da zunubi. Sannan kuma abu ne sananne ga kowanne mutum irin haxarin da qasashen musulmi suka faxa na fitsarar mata, da shiga ta rashin kunya da gujewa hijabi, da bayyana kwalliyarsu ga mazajen da ba nasu ba. Babu shakka wannan abu ne da yake jawowa al’umma fushin Allah da azabarsa idan ba su tashi sun gyara halinsu ba. Ya ku jama’ar musulmi, ku yi aiki da umarnin Allah, ku tilastawa matanku kyakkyawar shiga, da sutura ta musulunci, wanda hakan zai sa su sami kuvuta, ku ma ku kuvuta. Allah ta’ala yana cewa: (يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِنْ جَلَابِيبِهِنَّ ذَلِكَ أَدْنَى أَنْ يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَحِيمًا) [الأحزاب: 59] . (Ya kai wannan Annabi ka gayawa matanka da ‘ya’yanka mata, da matan muminai, su lulluve jikinsu da mayafansu, don da haka ne za a gane su, kuma ba za a cutar da su ba. Lallai Allah mai yawan gafara ne mai jinqai). A nan Allah ta’ala yana umartar mata musulmai da su lulluve jikinsu da sutura ta musulunci wato hijabi, ta haka ne za a gane cewa su mata ne kamammu. Ba za su fitini mutane ba da kyan da Allah ya yi musu, kuma su ma ba za a fitine su ba, ta hanyar maganar banza. Don haka ku ji tsoron Allah ya ku musulmai. Ku hana wawayenku yin wauta. Kuma ku hana matanku aikata abin da Allah ya haramta. Ku umarce su da sanya hijabi da sutura ta musulunci, kuma ku tsoratar da su fushin Allah. Kamr yaddda ya tabbata a hadisi, Imam Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi suka rawaito shi, daga Abubakar Siddiq (R.A), cewa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Lallai idan mutane suka ga azzalumi yana zalunci, kuma ba su hana shi ba, to ba da daxewa ba Allah zai lulluve su da uqubarsa.” Allah ta’ala Ya faxa a cikin littafinsa: (لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَى لِسَانِ دَاوُودَ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ذَلِكَ بِمَا عَصَوْا وَكَانُوا يَعْتَدُونَ78 كَانُوا لَا يَتَنَاهَوْنَ عَنْ مُنْكَرٍ فَعَلُوهُ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ79) [المائدة: ٧٨ – ٧٩]. (An la’anci waxanda suka kafirta daga cikin Banu Isra’ila, a kan harshen Dawud da Isa xan Maryam saboda savo da suka yi, kuma sun kasance suna qetare iyaka. Sun kasance ba sa hana junasu wani mummunan aiki da suka aikata, lallai tir da abin da suka kasance suna aikatawa). Kuma ya tabbata a hadisi wanda Imamu Ahmad ya rawaito daga Abdullahi xan Mas’ud (R.A), Annabi (S.A.W), ya karanta wannan ayar sai ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunsa, lallai ku yi umarni da kyakkyawan aiki, kuma lallai ku hana mummuna, kuma lallai ku tursasa shi ya bi gaskiya, idan ba haka ba kuwa, Ubangiji ya sassava tsakanin zuciyarku kuma ya la’ance ku kamar yadda Ya la’ance su”. Kuma ya tabbata daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya ga mummunan abu to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to ya sauya shi da harshensa, idan kuma ba zai iya ba to ya qi shi a zuciyarsa. Wannan shi ne mafi raunin imni”. Allah ta’ala ya umarci mata da zaman gida da daina yawace-yawacen shirme, Ya hana su karairaya murya ga mazajen da ba nasu ba, domin yin haka yana jawo fitina da varna. Allah ta’ala ya ce: (يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا 32 وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآَتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا) [الأحزاب: ٣٢ - ٣٣]. (Ya ku matan Annabi, ba daidai kuke da kowacce mace ba, idan kun ji tsoron Allah, don haka kada ku karairaya murya wajen magana sai wanda yake da cuta a cikin zuciyarsa ya yi kwaxayi. Kuma ku yi maganar da ta dace. Kuma ku zauna a cikin gidajenku kada ku yi tamvele irin tamvelen jahiliyyar farko, kuma ku bi Allah da manzonsa) . A cikin waxannan ayoyi masu girma Allah ta’ala ya yi hani ga matan Annabi, iyayen muminai waxanda su suka fi kowacce mace tsarkaka, da kada su karairaya muryarsu yayin magana ga mazajen da ba nasu ba, domin kada su ba wa wani mai mugun nufi dama har ya nemi maganar banza da su. Kuma ya umarce su da su zanuna a gidajensu kada su dinga cava ado suna bi gwadabe-gwadabe kamar matan jahiliyya na farko, domin yin haka shi yake haddasa zinace-zinace a cikin al’umma. To idan har Allah ta’ala zai faxawa matan Annabi iyayen muminai wannan maganar, ya ja kunnensu a wannan aya, tare da girman imaninsu da falalarsu da xaukakarsu, to kuwa babu shakka sauran mata muminai su ne suka fi cancanta a yi wa irin wannan gargaxi. Kuma Allah ta’ala ya ce: (وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِنْ وَرَاءِ حِجَابٍ ذَلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ53) [الأحزاب: ٥٣]. (Kuma idan za ku tambaye su wani abin amfani, to ku tambaye su ta bayan shamaki, yin haka shi ya fi tsarki ga zukatanku da kuma zukatansu). Wannan aya ta fito qarara ta nuna wajabicin mata su tsare kansu daga mazajen da ba nasu ba. Ta kuma nuna cewa yin haka shi zai magance aukuwar fitina tsakanin maza da mata. Ya ku bayin Allah lallai hijabin mace yana da sharuxxai guda takwas. Ga su kamar haka: Ya rufe dukkani jikin ‘ya mace, domin faxar Allah da yake cewa su lulluve jikinsu da mayafansu. Kada ya hijabin ya kasance shi karankansa kwalliya ne, wato a yi masa ado da launi iri-iri ko kayan ado na musamman ta yadda zai dinga jan hankalin maza. Allah ta’ala yana cewa: (وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَ 31)[النور: ٣١]. (Kuma kada su bayyana adonsu, sai dai abin da ya riga ya bayyan). Ma’anar abin da ya riga ya bayyana shi ne, adon da ya riga ya bayyana ba da gangan ba. Don haka, duk hijabi mai kwalliya to ba hijabi ba ne a musulunci. Ya kasance mai kauri ba shara-shara ba, yadda zai riga nuna jikin mace. Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira, (R.A) cewa, manzon Allah (S.A.W) ya ce; “Wasu mutane kala biyu ‘yan wuta ne, ban tava ganinsu ba, na farko wasu mutane a xauke da bulalai, tamkar jelar shanu, za su riqa dukan mutane da su, da kuma wasu mata sanye da tufafi amma tsirara suke, masu tafiya suna karairaya, suna rangaji, kawunansu kai ka ce tozon raquma ne masu rangaji. Faufau ba za su shiga aljanna ba, ba za su tava jin qanshita ba, ga shi kuwa qamshinta a na jiyo shi daga tafiya mai tsawon kaza da kaza”. Duk matar da za ta yi shigar da ba za ta rufe mata jikinta ba, kuma a na ganin gashin kanta a waje, ko a na ganin qwaurinta a fili, to irin waxanan mata ko su suna ganin sun sanya sutura, to tsirara suke yawo. Kuma an la’ance su, ba kuma za su shiga aljanna ba. Sharaxi na haxu: Hijabin ya zama burmeme mai faxi, ba matsattse ba, wanda zai riqa nuna hoton dirin mace ba. An karvo hadisi daga xan Usama xan Zaid, ya ce, mahaifinsa Usama ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya sanya min wata tufa mai kauri, wadda Dihya Alkalbi ya ba shi kyauta. Sai ni kuma na ba wa matata ta sa. Sai manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Me ya hana kai ba ka sa ta ba?” Sai na ce, matata na ba wa take sawa. Sai Annabi (S.A.W.) ya ce, “To ka umarce ta ta sa wata rigar a qasanta, domin ina jin tsoron ta riqa nuna dirinta”. Imam Ahmad ne ya rawaito shi. Kada hijabin ya zamana yana qanshin turare, saboda hadisai masu yawa da suka tabbata daga Manzo (S.A.W), yana hana mata fita suna qanshin turare. An karvo daga Abu Musa al-Ash’ari (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W), ya ce, duk matar da ta sa turare ta wuce ta gaban maza don su ji qanshinta, to karuwa ce”. Nasa’i da Xan Kuzaimah da Xan Hibban ne suka rawaito. Kada ya yi kama da tufafin maza. An karvo hadisi daga Abu Huraira, (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W), ya la’anci namijin da yake shigar mata, da kuma macen da take shigar maza. Abu Dawud ne da Nasa’i suka rawaito shi. Sharaxi na bakwai shi ne, kada ya yi kama da tufafin kafirai mata. Saboda a qa’idar shari’a ba ya halatta ga mace ko namiji su kwaikwayi shiga irin ta kafirai a lokutan ibadojinsu, ko kuma a lokutan idinsu, ko a suturunsu na yau da gobe. An karvo daga Abdullahi xan Umar (R.A), ya ce, manzon Allah (S.A.W), ya ce, “Duk wanda ya yi kama da wasu mutane to yana daga cikinsu. Imam Ahmad ne ya rawaito shi. Don haka ba ya dacewa ga ‘ya mace ta riqa yawo kanti-kanti da kaya irin na kafiran kasashen yamma don yin kwalliya da irinsu. Sharaxi na takwas, kada ya zama sutura ce ta shuhura. Ita ce duk wata shiga da mutum zai yi domin ya shahara da ita a gurin mutane. An karvo daga Abdullahi xan Umar (R.A) ya ce, manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda ya sanya taguwar shuhura a nan duniya, Ubangiji zai sanya masa taguwar qasqanci rana gove alqiyama, sannan ya babbaka shi da wuta.” Abu Dawud ne da Ibn Majah suka rawaito shi. Don haka, wajibi ne ga kowanne musulmi ya ga cewa, hijabin matarsa da na ‘ya’yansa mata sun cika waxannan sharuxxan, domin faxar ma’aiki (S.A.W) “Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowannenku za a tambaye shi game da abin kiwonsa”. Kuma Allah ta’ala yana cewa: (يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا قُوا أَنْفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَائِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَا يَعْصُونَ اللَّهَ مَا أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ6) [التحريم: 6] (Ya ku waxanda suka yi imani ku tsare kawunanku da iyalanku daga shiga wuta, mutane da duwatsu ne makamashinta. Mala’ikun da suke tsaronta mala’iku ne masu kaushin zuciya, qarfafa, ba sa savawa Allah a abin da ya umarce su, kuma suna aikata abin da ya sa su). Hakan nan, wajibi ne ga bawa ya ji tsoron Ubangijinsa, ya kiyayi sava masa, Allah ta’ala yana cewa: (قُلْ لِلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَلِكَ أَزْكَى لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ 30وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَى جُيُوبِهِنَّ31) [النور: ٣٠ – ٣١] (Kuma ka gaya wa muminai maza su kame ganinsu, kuma su kiyaye farjinsu, wannan shi ne ya fi tsaki gare su, lallai Allah mai yawan sani ne ga abin da suka aikatawa. Kuma ka gayawa muminai mata su kame ganinsu su kuma kiyaye farjinansu kada su bayyana adonsu ai abin da ya bayyana. Su rufe qirajansu da lulluvinsu). Ina nemawa kaina tare da ku da sauran muminai gafarar Allah daga kowanne zunubi, don haka ku nemi gafararsa, lallai shi mai yawan gafara ne mai jinqai
Dukkan yabo da kirari sun tabbata ga Ubangijin talikai, kuma kyakkyawan qarshe yana ga masu tsorn Allah. Babu ta’addanci sai a kan azzalumai. Tsirada amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta bakixaya, Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa, waxanda suka bi tafarkinsa har zuwa tashin qiyama. Bayan haka, ya ku bayin Allah, abu ne da kowa ya sani irin yadda mata a yau suke cava kwalliya da shiga irin ta fitsara da rashin kunya da sa matsattsun kaya, masu fito da al’aura. Suna yawo da su tsakanin mazaje. Al’amarin da yake haddasa fitintunu iri-iri da fasadi kala-kala a cikin al’umma. Haka nan yana daga cikin abubuwan da ke jawo fasadi, shi ne kevantar namiji da matar da muharramarsa ba. Alhali hadisi ya tabbata daga Abu Sa’idul Kudri (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W), ya ce: “Ba ya halatta ga macen da ta yi imani da Allah da ranar lahira, ta yi bilaguron mai tafiyar kwana uku ko fiya, face suna tare da maharraminta; babanta ko xan’uwanta, ko mijinta, ko kuma xanta, ko kuma kowane xaya daga muharramanta”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma Imamu Ahmad da Tirmizi da Hakim sun ruwaito hadisi cewa, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce, “Babu wani mutum da zai kaxaita da wani mace, face shaixan ne na ukunsu”. Ya ku Musulmi ku ji tsoron Allah, ku hana matanku shiga ta fitsara da watangaririya a cikin gari, da nuna kwalliya da tsiraici. Ku hana shiga irin ta maqiya Allah, Nasara da Yahudu, da masu kwaikwayonsu. Ku sani cewa, rashin magana a kan wannan sha’ani daidai yake da aikata, don haka idan uqubar Allah ta sauka, za ta shafi kowa da kowa. Allah ya tsare mu. Ya ku musulmi! Babu shakka cewa, nauyin da yake kan shugabanni da alqalai da malamai, da shugabannin qungiyoyi, ba qarami ba ne. Ya xara nauyin da yake kan wasu, kuma haxarin da yake cikin rashin maganar a kan wannan batu ba qaramin haxari ne ba. Duk da cewa, ya kamata a sani ba su kaxai ke da alhakin yin magana da tsawatarwa a kan wannan lamari ba. A’a, duk wani musulmi yana da ruwa da tsaki cikin fafutukar ganin an kawar da irin waxannan laifuka. Musamman dattawa da manyan gari, da iyayen matan su kansu, da mazajensu na aure. Dole ne duk a tashi tsaye wajen jan-kunne mai tsanani ga duk wacce za ta nemi yaxa irin wannan fasadi. Idan mun yi haka, to muna sa ran Allah zai yaye mana bala’in da muke ciki, ya shiryar da mu tare da matanmu daidaitaccen tafarki. Ya ke ‘yar uwa musulma. Ki ji tsoron Allah, ki komo kan hanya, tun gabanin ranar qin dillanci ba ta zo ba, ranar da ido zai rena fata. Ki sani azabar Allah mai tsanani ce. Kuma duniya ba matabbata ce ba. Ki kiyayi jin kunyar lahira gaban halittun farko da na qarshe. Allah ya datar da mu gabaxaya ga abin da yake so kuma ya yarda da shi. Kuma muna roqon Allah ya kare mana ‘yan matan muslmi daga kaidin masu kaidi, da dakon masu mugun nufi. Ka sanya su daga cikin mata salihai, masu koyi da salihan mata na gari, masu guje wa duk wata varna, masu aiki da Alqurani da Hadisan Ma’aiki (S.A.W.). Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangiji mai izza ga barin abin da suke siffantawa. Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni, kuma yabo da godiya da kirari su tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
Tags: