Tsawatarwa game da fitinar mata


5068
Surantawa
Yanzu mafi yawancin matanmu sun fice daga bin shiriyar addini miqaqqe da hanya madaidaiciya, sun koma bin bayyananniyar hanyar 'bata wadda za ta jefa su a cikin wutar hawiya. Shi yasa musulunci baiyi watawata ba wajen bayyana hatsarin hakan tare da kama hannunsu domin hanyar tsira.!

Manufofin huxubar

Riga kafin fitinar mata.

Tarbiyyantar da mata a kan kamun kai.

Tunatar da musulmai nauyin da ke kansu.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka: Haqiqa Allah ya umarci mutanen farko da na qarshe da jin tsoronsa, domin kuwa da dalilinta ne ake samun tsira da kuma rabautar duniya da ta lahira kamar yadda Allah maxaukakin sarki yake cewa:

( وَلِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَلَقَدْ وَصَّيْنَا الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَإِيَّاكُمْ أَنِ اتَّقُوا اللَّهَ وَإِنْ تَكْفُرُوا فَإِنَّ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَكَانَ اللَّهُ غَنِيًّا حَمِيدًا 131 ) [النساء: 131]

“Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qassai duk na Allah ne. Kuma haqiqa mun yi wa waxanda aka bai wa littafi gabaninku, da ku kanku wasiyya ku ji tsoron Allah. Idan kuwa kuka kafirce, to ku sani cewa (duk) abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qassai na Allah ne. Allah kuwa ya kasance mawadaci ne sha-yabo”.

Sai Allah ya yi umarni da jin tsoronsa, wanda shi ne kariyar afkawa zuwa kowace irin fitina, abin nufi da cewa a ji tsoronsa shi ne, a aikata umaninsa, kuma nisanci haninsa, a fili fa voye. Kuma wannan umarni da Allah ya yi ya shafi gabaxayan bayinsa; mazansu da matansu, sai dai maza su ne waxanda suke tsaye a kan al’amuran mata, don haka ya zama dole a kansu su xora mata a kan jin tsoron Allah mai girma da buwaya ta kowace hanyar tarbiyya wadda shari’a ta yarda da ita. Allah ya fifita maza a kan mata saboda abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu, da kuma cikar hankalisu da hangen nesansu a cikin al’amura, da ma wasun waxannan abubuwan. Allah Maxaukaki Ya ce:

( الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْضٍ وَبِمَا أَنْفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ ) [النساء: 34].

“Maza sama suke da mata saboda abin da Allah ya fifita sashinsu (da shi) bisa sashi, da kuma abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu”.

Malam Shanqixi Allah ya rahamshe shi, ya ce a qarqashin tafsirin wannan aya: “Allah ya yi nuni da cewa namiji ya fi mace, saboda kasancewa namiji xaukaka ce da cika, matanci kuwa a asali, xabi’a ce ta tawaya. Kuma duk halittu sun haxu a kan haka, domin kuwa za ka ga gabaxayan mutane suna sanyawa mace dukkan nau’o’in kayan ado da kwalliya, wannan kuwa yana nuna qoqarinsu ne na cike tawayar matanci. Savanin namiji, wanda kasancewarsa namiji kaxai ya wadatar da shi daga qaye-qayen kwalliya da makamantan haka. Umarni da tsoron Allah ya shafi umartar kai da kuma iyalai, kuma maza su aka xorawa tsayuwa a kan mata saboda fifikon matsayinsu a kansu.

Sannan kuma abu ne a fili gare mu gabaxaya cewa, halin da mata muslmai ke ciki a yau ya sava da irin halin da matan musulmai suke kai a lokacin Manzon Allah, (ﷺ). Matanmu a yau sun zavi hanyar ‘yan ba ruwanmu da addini, don haka da su suke koyi sau da qafa kamar dai yadda hadisi ya ambata, yanzu mafi yawancin matanmu sun fice daga bin shiriyar addini miqaqqe da hanya madaidaiciya, sun koma bin bayyananniyar hanyar vata wadda za ta jefa su a cikin wutar hawiya! Allah ka tsare mu, amin.

Kuma wannan savawa da mata suka yi hotonsa na fitowa fili ne ta salo daba-daban, manya daga cikinsu su ne:

Cakuxuwarsu da maza a ma’aikatun hukuma, da qananan makarantu da manya. Da kuma cakuxexeniyar maza da mata a kasuwanni da motocin haya da makamantan haka, alhaku kuwa duk wannan haramun ne, Allah maxaukaki ya ce:

( وَلَمَّا وَرَدَ مَاءَ مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةً مِنَ النَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِنْ دُونِهِمُ امْرَأتَيْنِ تَذُودَانِ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا قَالَتَا لَا نَسْقِي حَتَّى يُصْدِرَ الرِّعَاءُ وَأَبُونَا شَيْخٌ كَبِيرٌ23 فَسَقَى لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّى إِلَى الظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّي لِمَا أَنْزَلْتَ إِلَيَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ24فَجَاءَتْهُ إِحْدَاهُمَا تَمْشِي عَلَى اسْتِحْيَاءٍ قَالَتْ إِنَّ أَبِي يَدْعُوكَ لِيَجْزِيَكَ أَجْرَ مَا سَقَيْتَ لَنَا فَلَمَّا جَاءَهُ وَقَصَّ عَلَيْهِ الْقَصَصَ قَالَ لَا تَخَفْ نَجَوْتَ مِنَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ25 ) [القصص: 25].

(Lokacin kuma da (Annabi Musa) ya gangara wajen ruwan Madyana sai ya sami wasu mutane masu yawa suna shayar (da dabbobinsu), kuma ya sami wasu mata su biyu a gefensu suna tsare dabbobinsu, sai ya ce (da su) “Me ya same ku ne”? Sai suka ce: “Mu ai ba ma shayarwa har sai duk makiyayan sun juya, kuma mahaifinmu tsoho ne tukuf”. To sai ya shayar musu (da dabbobin nasu) sannan ya koma wurin wata inuwa ya ce, “Ya Ubangijina haqiqa ni mavuqace ne ga abin da ka saukar zuwa gare ni na alheri”. Sai xayarsu ta zo masa tana tafiya cikin kunya ta ce: “Babana yana kiran ka don ya saka maka ladan shayarwar da ka yi mana”. To lokacin da ya zo wurinsa ya kuma ba shi labarin (abubuwan da suka faru da shi) sai ya ce da shi, “Kada ka ji tsoro, ka tsira daga azzaluman mutane”).

Ya ‘yan uwa! Ku yi tunani a kan irin wannan matsayin da waxannan ‘yan mata suka xauka. Sannan kuma a auna shi da abubuwa da suke faruwa a yau.

Bayan haka: An karvo daga Abdullahi bn Amr, daga Manzon Allah, (ﷺ) ya ce: “Ku umarci ‘ya’yanku da salla suna ‘yan shekara bakwai, ku kuma dake su a kan sakaci da ita idan suna ‘yan shekara goma, sannan kuma ku raba tsakaninsu a wajen kwanciya”. Abu Dawud da Hakim ne suka rawaito shi.

Wannan hadisi yana nuni a kan cewa haqiqa musulunci ya haramta cakuxar maza da mata, kuma yana ba da tarbiyya a kan kame kai tun a lokacin yarinta.

Halin kuwa da mafi yawan mata suke kai a yau na savawa dokokin shari’a, irin su cakuxuwa da maza a kasuwanni, da xaga murya da wasun haka, gyransu haqqi ne da yake wuyan kowa, don haka ya zama dole kowa ya tsayu da sauke nasa nauyin ko da yake hukuma ita ta fi kowa kaso mafi yawa.

Bayyanar da ado ma, da fitar da sassan jiki, da suke motsa sha’awa su kuma haifar da varna su ma na daga cikin gagga-gaggan savo. Domin kuwa su ne hanyar da ke sadarwa zuwa ga zina. Ga shi kuwa Allah ya yi umarni da sa hijabi kuma ya ce, a rintse idanuwa, kuma yana hana fitar maguzanci. Allah maxaukakin sarki yana cewa:

( قُلْ لِلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَلِكَ أَزْكَى لَهُمْ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ30وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَى جُيُوبِهِنَّ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آَبَائِهِنَّ أَوْ آَبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ أَوْ نِسَائِهِنَّ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُنَّ أَوِ التَّابِعِينَ غَيْرِ أُولِي الْإِرْبَةِ مِنَ الرِّجَالِ أَوِ الطِّفْلِ الَّذِينَ لَمْ يَظْهَرُوا عَلَى عَوْرَاتِ النِّسَاءِ وَلَا يَضْرِبْنَ بِأَرْجُلِهِنَّ لِيُعْلَمَ مَا يُخْفِينَ مِنْ زِينَتِهِنَّ وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَا الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 31 ) [النور: 31].

(Ka ce wa muminai maza, su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lallai ne Allah, Masani ne ga abin da suke aikatawa. Kuma ka ce wa muminai mata, su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana adonsu, face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna adonsu face ga mazansu ko ubanninsu, ko ubannin mazansu, ko ‘ya’yansu ko xiyan mazansu, ko ‘yan’uwansu ko ‘yan’yan ‘yan’uwansu, ko ‘yan uwansu maza, ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata, ko matansu, ko qwaraqwaransu, ko mabiya, ba masu buqatar mata ba daga maza, ko qananan yara waxanda ba su tsinkaya a kan al’aurar mata. Kuma kada su yi duka da qafafunsu, domin a san abin da suke voyewa daga adonsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya, ya ku muminai. Tsammaninku, ku sami babban rabo).

Kiyaye farji, yana iya nufin rufe tsiraici, da kuma nisantar zina.

Imamu Ahmad da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Huraira ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Sanfirin mutane biyu ‘yan wuta ne, har yanzu ban gan su ba. (Na farkonsu) wasu jama’a xauke da bulalu kamar jelar shanu suna dukan mutane da su, da kuma wasu mata sanye da sutura amma kuma suna tsirara, masu karkataccen hali, masu kwarkwasa, kawunansu kamar karkataccen tozon raqumi, ba za su shiga aljanna ba kuma ba za su ji qamshinta ba, ga shi kuwa ana jiyo qamshinta tun daga nisan kaza da kaza.

Xan Abdulbarri ya ce: “Manzo Allah (ﷺ) yana nufin matan da suke sa shara-sharan kayan da suke siffata jiki kuma ba sa suturce shi, a suna sun sa sutura, amma kuma a haqiqance kuma tsirara suke. Karkatattu daga bin gaskiya, kuma masu karkatar da mazajensu daga gaskiya. ‘Yan uwa a yi hattara.

Malamai sun yi bayanin abin da ake nufin da (Sanye da kaya, kuma tsirara) cewa, ita ce macen da take sa shara-sharan kayan da ba za su rufe mata tsiraici ba, ko matsattsun kayan da suke bayyana sassan halittarta. Alhali kuwa suturar mace a shari’ance ita ce wadda take suturce ta, ba tare da ta bayyanar da jikinta ba, ko wata gava daga cikin gavvanta ba, saboda kaurin kayan da kuma yalwarsu.

Wannan shi ne abin da ya sauqaqa. Allah ya yi mana gafara ni da ku da sauran musulmi bakixaya. Lalle shi mai karvar gafara ne mai jin qai.

Huxuba Ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta baki xaya, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya bi shiriyarsa, kuma ya yi riqo da sunnarsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Haqiqa matan magabata Allah ya rahamshe su, masu kamun kai ne, masu sanya hijabi ne, masu kuma biyayya ga Ubangijin talikai ne, a duk abin da aka umarce su. Mu kalli labarin qagen da aka yi wa Nana A’isha. Labarin ya bayyana cewa A’isha ba ta yi wa wannan sahabi magana ba, (wato Safwan Ibn Mu’axxil), kuma shi ma ko kalma bai ce mata ba, sai dai ji ta yi yana cewa, inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, a yayin da ya gan ta haka dai har suka iso Madina.

A yayin da aka yi umarni da hijabi nan take suka rungume shi da gaggawa.

Ya zo a cikin ingantaccen hadisi daga Ummu Salama ta ce: Yayin da wannan ayar ta sauka:

( يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِنْ جَلَابِيبِهِنَّ ) [الأحزاب: 59].

(Su yafa mayafansu).

Matan Madina sai suka rinqa fita kamar masu xauke da hankaki a kansu, saboda nutsuwa, suna sanye da baqaqen tufafi. Allahu Akbar, ka ji gaggawar amsa umarnin Allah da na Manzonsa.

An karvo daga Ummu Salama ta ce, wata mace ta ce da ita: “Ni mace ce da nake tsawaita levatun suturata, kuma nakan wuce ta gurin da yake da qazanta. Sai ta ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Abin da yake biye da shi yana tsarkake shi”. Malik da Ahmad da Tirmizi da Abu Dawud da kuma Darimi ne suka rawaito shi.

Malam Baji, ya ce: “yayin da suka bi umarnnin da aka yi musu, kuma suka hanu daga hanin da aka yi musu sai Allah ya tsare su daga fitintinu da bala’ai na duniya da lahira kuma ya tanadar musu da lada mai girma.

Matan magabata sun sami tarbiyyar kamun kai, da kunya da aiwatar da umarni tare da nisantar hani, don haka muna da kyakkyawan abin koyi game da su, amma fa ga wanda yake fatan haxuwa da Allah da manzo da ranar lahira sumul qalau.

Ya bayin Allah! Idan fa muka bar matanmu da ‘ya’yanmu ba nusarwar qwarai zuwa ga Ubangiji, ba shakka za su faxa cikin halaka.

Allah dai ya sanya maza su zama tsayayyu a kan mata. Su kuma mata ya yi su masu raunin hankali da addini don haka ne ma manzo ya yi wasiyyar alheri game da su. Kamar yadda yake a cikin hadisin Amr xan Ahwas al-Jushami, Allah ya yarda da shi ya ce, Haqiqa ya ji Annabi (ﷺ) a hajjin ban kwana yana cewa, bayan ya godewa Allah ya yi masa kirari kuma ya tunatarwa, ya yi gargaxi sannan sai ya ce: “Ku saurara ku yi wasiyyar alheri ga mata, haqiqa su mataimaka ne gare ku". A wani lafazin hadisin. “………..Haqiqa an halicci mace ne daga qashin haqarqari, kuma mafi kantarar qashin haqarqarin mafi xaukakarsa, in ka tafi miqar da shi ka karya shi in ka bar shi kuma ba zai daina karkata ba, don haka ku yi wa mata wasiyya. Manzo Allah ﷺ) ya keve mata da cewa, a yi musu wasiyya ne saboda rauninsu da kuma buqatuwasu ga wanda zai tsayu a kan tafiyar da al’amuransu. Shi ya sa ya ce, ku karvi wasicina game da su, kuma ku yi aiki da ita, ku kuma yi haquri da su ku tausasa musu kuma ku kyautata musu. Babu shakka idan mace ta rasa nusarwa za ta iya zama shaixaniyar kanta, kuma vatacciya mai vatar da mutane daga hanya maidaidaiciya. Hatta karuwan da ake da su a yau, sun isa shaida kan yadda macen da ta rasa saiti da nusarwa take zama. Ya ‘yan’uwa! Wannan bai isa ya sa mu faxaka ba?

Don haka ya ke 'yar uwata musulma, ki ji tsoron Allah, ki qanqame addininki, ki yi riqo da musuluncinki, kuma ki yi alfahari da riqo da addininki. Ki xaga kanki sama a ko ina. Kuma ki guji kuraye masu fuskokin mutane, rundunar Iblis, waxanda suke nemanki ruwa a jallo su faruto ki cikin ruwan sanyi, sannan su halaka ki a tsanake. Ko da yaushe kasance tare da littafin Allah da sunnar Annabi (ﷺ). Ki yi koyi da raywar matan farko na qwarai daga matan sahabbai da tabi'ai. Idan kin yi haka za ki samu rabauta da gidan aljanna, da yardar Allah.

Tags: