Abota Ta Kwarai Da Tasirinta Ga Mutum


8007
Surantawa
Bayan haka: Ya bayin Allah! Haqiqa musulunci addni ne da yake da nagartattun 'dabi’u, don haka ya dace da 'dabi’un da ba a gur'bata su ba. Ya kuma dace da 'dabi’un da suke masu kyawu. Musulunci shi ne maganin gur'batattun 'dabi’u

Manufofin huxubar

Tarbiyyantar da musulmi a kan al’adun musulunci.

Umarni da abokantakar mumina na qwarai da nisantar miyagun abokai.

Mai da hankali a kan tarbiyyar ‘ya’ya mata da sa ido a kan qawayensu.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka: Ya bayin Allah! Haqiqa musulunci addni ne da yake da nagartattun xabi’u, don haka ya dace da xabi’un da ba a gurvata su ba. Ya kuma dace da xabi’un da suke masu kyawu. Musulunci shi ne maganin gurvatattun xabi’u, kamar yadda ya tabbata a hadisin da Bukhari da Muslim suka rawaito na Abu Huraira mai xauke da cewa: “Duk wani xa asali ana haihuwarsa ne a kan xabi’un qwarai, sai dai iyayensa su Yahudantar da shi, ko su Kiristantar da shi, ko kuma su maguzantar da shi”.

Kamar yadda aka halittawa Annabi Adamu, Hawwa’u don ya sami nutsuwa da hutu da ita, Allah bai bar shi, shi kaxai ba. Allah Ya ce:

(هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيْهَا189) [الأعراف: ١٨٩].

(Allah shi ne wanda ya halicce ku daga rai xaya (shi ne Annabi Adam) ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami nutsuwa da ita).

Musulunci ya yi aiki tuquru don tabbatar da wanna kyakkyawar xai’a ta rayuwa tare da mutane. Don haka hukunce-hukuncensa dadama suka qunshi tattaruwa cikin jama’a da gudanar da su tare. Kamar sallar Juma’a, jam’in salloli, da idi biyu da kuma sallar kisfewar rana ko wata.

Yana daga abubuwanda ke qara bayyana mana haka qarara a fili yunqurin da Annabi (ﷺ) ya yi na qone gidajen marasa zuwa jam’in salla. An karvo daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi ya ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Tabbas da na yi niyyar na sa ladani ya kira sallah, sannan in umarci wani ya jagoranci yi wa mutane salla, ni kuma in tafi da wasu jama’a xauke da xaurin itatuwa zuwa ga waxanda ba sa zuwa salla a jam’I, in qone gidajensu da wuta". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Haka kuma Manzo (ﷺ) ya kwaxaitar da matafiyi a kan yin tafiya a cikin ayari, ya kuma kira matafiyin da yake tafiya shi kaxai da shaixani. Kamar yadda ya zo cikin hadisin Abdullahi xan Amr cewa, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Matafiyi shi xaya jal shaixani ne, matafiya su biyu kuma shaixanu biyu ne, matafiya uku kuwa sun zama ayari. Maliku da Tirmizi da Abu Dawud da Nasa’i ne suka rawaito shi, Sheikh Albani kuma ya inganta shi.

Bisa ga xabi’ar mutum, yana son binnanci, kuma ba ya so rayuwa shi kaxai, don haka yake jin kamar ya zamar masa dole a sami taimakekeniya a tsakaninsa da wani, kamar yadda ya zamar masa dole ya yi hulxa tare da wasu. Kwatsam sai musulunci ya zo ya qarfafi wannan xabi’a ya shar’anta wasu ibadu da ba a yinsu sai a cikin ayari, kamar irin su sallar jam’i da juma’a da idi biyu da sauransu.

Yana daga tilas xin rayuwa, shi ne, mutum ya zavawa kansa abokin hulxa tare da shi, wanda zai riqa nusar da shi da tunatar da shi a duk lokacin da ya shagala ko ya manta. Wanda kuma zai riqa sanar da shi abin da ya jahilta.

Kuma a kodayaushe akan gane mutum ne da abokin hulxarsa. Kamar yadda wani mawaqi yake cewa: Ina kana son ka san mutum to kalli abikinsa. Duk aboki da abokinsa yake koyi. Idan abokin asharari ne to maza ka guje shi, idan kuwa na kirki ne to ka matse shi, sai ka shiriya.

Ya bayin Allah! Haqiqa Allah ya shar’anta mana qaunatarsa da qaunatar manzonsa da kuma muminai, kuma tabbatuwar hakan na daga mafi qarfin igiyar imani.

Kamar yadda Allah ya tilasta mana yin qiyayyar duk wani abu da ya sava Allah da Manzonsa. Allah maxaukaki yana cewa:

(إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آَمَنُوا الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلَاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ55 وَمَنْ يَتَوَلَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَالَّذِينَ آَمَنُوا فَإِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْغَالِبُونَ56) [المائدة: ٥٥ – ٥٦].

(Haqiqa Allah ne majivincin al’amuranku da Manzonsa da kuma muminai waxanda suka ba da gaskiya, waxanda kuma suke tsai da salla da ba da zakka, suna masu qanqantar da kai, duk kuwa wanda ya jivinci Allah da manzonsa da kuma waxanda suka ba da gaskiya, to haqiqa rundunar Allah su ne masu rinjaye).

Yana daga cikin amfanin imani da waxandann ayoyi zavawa kai abokan qwarai. Allah ya ce:

(لَا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآَخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آَبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءَهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ22) [المجادلة: ٢٢].

(Ba za ka sami mutanen da suka ba da gaskiya da Allah da ranar lahira ba suna qaunar waxanda suke gaba da Allah da manzonsa ba, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne, ko ‘ya’yansu, ko ‘yan uwansu ko kuma danginsu).

Irin abin da wannan aya ta qunsa na tsawatarwa da hani kan qaunata da jibintar maqiyan Allah da manzonSa ya zo a wasu ayoyin daban kamar faxin Allah Maxaukaki:

(قَدْ كَانَتْ لَكُمْ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ فِي إِبْرَاهِيمَ وَالَّذِينَ مَعَهُ إِذْ قَالُوا لِقَوْمِهِمْ إِنَّا بُرَآَءُ مِنْكُمْ وَمِمَّا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ كَفَرْنَا بِكُمْ وَبَدَا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةُ وَالْبَغْضَاءُ أَبَدًا حَتَّى تُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَحْدَهُ4) [الممتحنة: ٤].

“Haqiqa kyakkyawan abin koyi ya kasance a gare ku game da (Annabi) Ibrahim da waxanda suke tare da shi, lokacin da suka ce da mutanensu, ba mu ba ku kuma, ba mu ba abin da kuke bauta wanda ba Allah, mun kafirce muku kuma qiyayya da gaba sun bayyana tsakaninmu da ku har abada sai sanda kuka ba da gaskiya da Allah Shi kaxai”.

Da kuma faxin Allah:

(مُحَمَّدٌ رَسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ29) [الفتح: ٢٩].

(Muhammadu Manzon Allah ne, kuma waxanda suka ba da gaskiya da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne).

Da kuma faxinsa:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا مَنْ يَرْتَدَّ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَسَوْفَ يَأْتِي اللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُ أَذِلَّةٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى الْكَافِرِينَ54) [المائدة: ٥٤].

(Ya ku waxanda kuka ba da gaskiya, duk wanda ya yi ridda daga cikinku ya bar addininsa to da sannu Allah zai zo da wasu mutane da yake son su, su ma suke son sa, masu qasqantar da kai ga muminai, masu tsananta wa kafirai).

Da kuma faxinsa:

(يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا قَاتِلُوا الَّذِينَ يَلُونَكُمْ مِنَ الْكُفَّارِ وَلْيَجِدُوا فِيكُمْ غِلْظَةً وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ مَعَ الْمُتَّقِينَ123) [التوبة: 123]

(Ya ku waxanda suka yi imani ku yaqi kafiran da suke kusa da ku, kuma su sami tsanani daga gare ku).

Da kuma faxinsa:

(يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ جَاهِدِ الْكُفَّارَ وَالْمُنَافِقِينَ وَاغْلُظْ عَلَيْهِمْ9) [التحريم: ٩].

(Ya kai wannan Annabi ka yaqi kafirai da munafuqai, kuma ka tsananta musu).

Da dai wasu ayoyi daban-daban waxanda ba waxannan ba.

Ke nan waxannan nassoshi na bayyana mana wajabcin riqar abokan qwarai da yin watsi da miyagun abokai.

Ya bayin Allah! A kodayaushe mai hankali yana gujewa miyagun abokai, kamar yadda yake gujewa zaki saboda ya san babu alheri tare da su, kuma duk wanda ke zama da su ya haxu da tavewa. Bisa ga misali kalli faxin Allah maxaukaki:

وَيَوْمَ يَعَضُّ الظَّالِمُ عَلَى يَدَيْهِ يَقُولُ يَا لَيْتَنِي اتَّخَذْتُ مَعَ الرَّسُولِ سَبِيلًا27 يَا وَيْلَتَى لَيْتَنِي لَمْ أَتَّخِذْ فُلَانًا خَلِيلًا28 لَقَدْ أَضَلَّنِي عَنِ الذِّكْرِ بَعْدَ إِذْ جَاءَنِي وَكَانَ الشَّيْطَانُ لِلْإِنْسَانِ خَذُولًا29 )[الفرقان: ٢٧ – ٢٩].

(Ranar da azzalumi zai riqa cizon yatsunsa yana cewa: “Kaicona ina ma na bi hanya tare da Manzo! Kaicona ina ma da ban riqi wane aboki ba? Haqiqa ya vatar da ni daga bin Alqur’ani bayan ya zo mini». Kuma shaixan ya kasance mai tavar da mutane ne).

Sannan kuma haqiqa Manzon Allah (ﷺ) a lokaci guda ya kwaxaitar da al’umma a kan zama da abokan qwarai, ya kuma tsawata a kan zama da miyagun abokai. Kamar a cikin hadisin da aka karvo daga Abu Musa Allah ya yarda da shi ya ce: Haqiqa manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kwatankwacin zama da abokin qwarai, da mugun aboki kamar zama da mai sayar da turare ne, da zama da maqeri. shi mai sayar da turare ko dai ya sam maka, ko ka saya, ko kuma ka ji qamshi. Shi kuwa maqeri ko dai ya qona maka sutura, ko kuma ka ji qauri”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Malam Muhallab ya ce: “A cikin wannan hadisin akwai bayanin albarkar zama da mutanen kirki. Da ambaton aikin alheri. Da kuma qara qaimi a kan yin aikin qwarai. Don haka ne ma Manzo ya yi umarni da zama da malamai da kuma lazimtar guraren ambaton Allah. Manzo (ﷺ) ya kwatanta abokin qwarai da mai sayar da turare wanda idan bai sam maka ba, to ba za ka rasa jin qamshi ba".

Ba ku ji abin da Luqmanu ya ce wa xansa ba: “Kai xana ka zauna da malamai, kuma ka matse su da gwiwoyinka, haqiqa Allah na raya zukata da hasken hikima kamar yadda yake raya qeqasasshiyar qasa da ruwan sama".

Ya kuma cewa, da shi: “Mai yiwuwa ne ka dace da samun rahama idan rahama ta sauka gare su, (wato su malaman), wannan shi ne amfanin zama da masu martaba da yin kicivis da su".

Haka ma malam Aini ya samo bayani daga wani malami cewa: “Ka zauna da wanda zamanka da shi zai sa ka qaru a addininka, ko ka qaru da ilimi, ko aikin qwarai da ake yi, ko kuma wata kyakkyawar xabi’a da yake da ita. Haqiqa idan mutum yana zama da wanda zama da shi ke sa shi tuna lahira, to kuwa ba makawa Allah zai datar da shi da samun wani gwargwado na alherin da hakan ke samarwa. To in kuwa haka ne yi qoqari ka sami abokin zaman zikiri da karatun Alqur’ani. Abin nufi dai hana zama da wanda za a cutu da zama da shi a addinince, ko kuma a duniyance. Sannan kuma da kwaxayin zama da wanda za a qaru da shi a addini da rayuwa".

Shi ma wani bawan Allah ya ce: “Ka nisanci mugun aboki, ka datse igiyar alaqa da shi, idan kuwa ba yadda ka iya da shi, to ka san dabarar zama da shi. Ka nace wa abokin kirki ka guji jayayya da shi, ka dace da samun tatacciyar qauna, matuqar dai ba za ka yi ja-in-ja da shi ba. Duk mutumin da ke yin abin kirki ga wanda kirki bai dame shi ba, to kuwa zai tarar da abin kirkin da ya yi a banza an yi watsi da shi. Allah yana da aljanna mai faxin sammai, sai dai fa kuma a zagaye take da abubuwan qi.

Ya Allah! Ka gafarta min dukkanin zunubina, da na masu sauraro na, da na dukkan musulman duniya gabaxaya, haqiqa kai mai yawan gafara mai yawan jinqai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bi hanyarsa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Ya bayin Allah! Babu shakka ribar abokantakar qwarai a bayyane take, a fili qarara ga xaixaiku, da ayarin jama’a, kuma daga haka ake samun nagartar daidaituwa, daga mutum xaya da jama’a. Samuwar nagartar jama’a shi ke yawaita albarkatun da Allah ke yin buxinsu ta sama da qasa, kamar yadda Allah ya ce game da mutanen alqaryu:

(وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آَمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ وَلَكِنْ كَذَّبُوا فَأَخَذْنَاهُمْ بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ96) [الأعراف: 96]

(Da dai mutanen alqaryu sun ba da gaskiya sun kuma ji tsoron (Allah) to ba shakka da mun buxe musu qofofinn albarkatai ta sama da kuma qasa, sai dai sun qaryata, sai muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa).

Imamul Baghawi ya ce: “Wato da an yi ta saukar da ruwan sama, kuma a yi ta fitar da tsirrai daga qasa, a kuma yaye fari da yunwa”.

Ya ‘yanuwa! Dukkanin ‘yan aljanna abokan qwarai ne, kamar yadda Allah maxaukaki ya ce:

(إِنَّ الَّذِينَ آَمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَانَتْ لَهُمْ جَنَّاتُ الْفِرْدَوْسِ نُزُلًا107) [الكهف: 107]

(Haqiqa waxanda suka ba da gaskiya, suka kuma yi ayyuka na gari to aljannar firdausi ce mmasaukinsu).

Da kuma faxinsa:

(وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِمْ مِنْ غِلٍّ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهِمُ الْأَنْهَار43)ُ [الأعراف: ٤٣].

(Kuma mun zare abin da yake cikin zukatansu na qullata qoramu suna gudana ta qarqashinsu).

Kuma dai Allah yana cewa:

وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِمْ مِنْ غِلٍّ إِخْوَانًا عَلَى سُرُرٍ مُتَقَابِلِينَ47 لَا يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَبٌ وَمَا هُمْ مِنْهَا بِمُخْرَجِينَ48)

“Muka cire abin da ke cikin zukatansu na qullata (suka zama) ‘yan uwa (suna) bisa gadaje suna fuskantar juna. Wata cuta ba za ta same su ba, kuma ba za a fitar da su daga cikinta ba”.

Ya bayin Allah! Haqiqa magabata Allah ya jiqansu da rahama sun fahimci wannan batu yadda ya kamata kuma sun ba shi cikakkiyar kulawa kamar yadda Annabi ya raine su a kan hakan.

Imamul Bukhari ya rawaito hadisi cikin sahihin littafinsa, wanda aka karvo shi daga Abi Juhaifa ya ce manzon Allah ya qulla ‘yan uwanta tsakanin Salman da Abid Darda’i, sai Salman ya ziyarci Abid Darda’i, sai ya ga Ummid Darda’i, daqal-daqal, sai ya ce da ita, “Ke kuwa me ya same ki”? Ta ce: “Xan uwanka Abud Darda’i ba shi da buqatar duniya” (wato bai damu da mace ba). Sai Abud Darda’i ya zo, sai ya dafa masa abinci sannan ya ce masa, “Ci abinci, ni ina azimi”. Sai shi kuma ya ce, “Ba zan ci ba har sai in ka ci”. Sai ya ci. Da dare ya yi sai Abud Darda’i ya tafi yin tsaiwar dare, sai Salman ya ce da shi, “Kwanta ka yi bacci”. Sai ya kwanta ya yi barci. Sannan ya kuma tafiya zai yi tsaiwar dare, sai ya qara cewa da shi, “Kwanta ka yi barci”. Yayin da kashin qarshe na dare ya shiga, Salman sai ya ce: “Tashi yanzu”. Sai suka tsahi suka yi sallah. Sai Salman ya ce da shi: “Tabbas Ubangijinka yana da haqqi a kanka, iyalanka ma suna da haqqi a kanka, to ka bai wa duk wani mai haqqi haqqinsa”. Sai ya je wajen Annabin ya ambata masa haka, sai Annabin (ﷺ) ya ce: “Salman ya yi gaskiya”.

Ku duba ku gani- ya bayin Allah-! Ya ya suka kasance suna taimakon juna a kan abin kirki da tsoron Allah, to haka fa ‘yan’uwantaka ta gari take.

Ya bayin Allah! Ku sani haqiqa duk inda watsattsun abokai suke ba sa wani abin kirki, sai dai su hana ka bin hanyar Allah. Bisa ga misali, kalli labarin mutuwar Abu Xalib, da irin yadda miyagun abokai suka hana shi yin imani. Ya zo cikin littafin Bukhari, an karvo daga Sa’id xan Musayyib, daga babansa, Allah ya yarda da shi, ya ce, "Yayin da mutuwa ta zowa Abu Xalib, Manzon Allah (ﷺ) ya zo wajnsa, sai ya tarar da Abu Jahil, da Abdullahi xan Abu Umayya xan Mugirah, sai ya ce: “Ya baffa! Ka ce, La’ilaha illal lah, kalma ce da zan tsaya maka a dalilinta a wajen Allah”. Sai Abu Jahil da Abdullahi xan Umayya suka ce: “Yanzu a ce ka qyamaci addinin (babanka) Abdulmuxxalib?!” Manzon Allah bai gushe ba yana bijirar masa kalmar shahada, su kuma suna maimaita faxa masa abin da suka faxa, har dai Abu Xalib a qarshen ya ce musu “Ina nan kan addinin (babana) Abdulmuxxalib”. Ya qi faxar La’ilaha ilal lah. Manzon Allah ya ce: “Wallahi zan nema maka gafarar Allah matuqar dai ba a hana ni nema maka ba”. Sai Allah ya saukar da faxarsa: مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ (وَالَّذِينَ آَمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ113) [التوبة: 113]

(Bai kamata ba ga Annabi da waxanda suka yi imani su riqa nema wa mushirikai gafara, koda kuwa makusanta ne, bayan sun gane cewa su ‘yan wuta ne).

Kuma Allah ya saukar da aya mai zuwa a kan batun imanin Abi Xalib sai ya ce da ManzonSa (ﷺ):

(إِنَّكَ لَا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ56) [القصص: ٥٦].

(Haqiqa kai ba za ka iya shiryar da wanda kake so ba, sai dai Allah yana shiryar da wanda ya so).

Ya ku iyaye dukkaninku makiyaya ne, kuma kowannenku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa. Kuma Manzon Allah (ﷺ) yana cewa: “Babu wani bawa da Allah zai ba shi kiwon wasu ababen kiwo a wayi gari ya mutu a ranar mutuwarsa yana mai ha'intar ababen kiwonsa, face sai Allah ya haramta masa shiga aljanna”.

Haqiqa yana daga cikin ha'inci, uba ya bar xansa sasakai ba ya tambayar ina xansa ya tafi, a ina ya kwana, kuma tare da wa yake kai kawo, sannan kuma uba bai san xansa yana karaxe gari daddare da shaixanun mutanen da suke savule masa addininsa da kuma gurvata masa hankali ba.

Don haka ahir da miyagun abokai, da kuma mugayen abokan zama. Dole ne a kan matsahi ya zavi abokan qwarai daga mutanen kirki masu hankali da nagarta waxanda za su riqa taimaka masa a kan gaskiya kuma suna nuna masa ita.

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaixan la'ananne:

(مَنْ عَمِلَ صَالِحًا فَلِنَفْسِهِ وَمَنْ أَسَاءَ فَعَلَيْهَا وَمَا رَبُّكَ بِظَلَّامٍ لِلْعَبِيدِ46) [فصلت: 46]

(Duk wanda ya yi aiki nagari, to kansa ya yi wa, wanda kuma ya munana a kansa ya yi wa, Ubangijinka ba mai zaluntar bayi ba ne).

Tags: