Bin iyaye da barin saba masu


5877
Surantawa
Haqqin haqqin iyaye yana nan daram, kuma zamantakewa tagari dasu wajibi ne, koda kuwa sun kasance kafirai, hakanan musulunci ya tsawatar daga saba masu matukar tsawatarwa, don haka ya sanya saba masu daga cikin mafi girman lefuka bayan shirka da Allah madaukakin sarki, kai har ma musulunci ya fifita hadimar iyaye akan jihadi wajen daukaka Kalmar Allah, wanda shine kololuwar musulunci.

Manufofin huxubar

Umarni da bin iyaye da falalarsa a addinin musulunci.

Umarni da kyautata wa iyaye koda kafirai.

Bayanin yadda ake bin iyaye da kyautata musu.

Jan – kunne kan savawa iyaye.

Bayyana makomar savawar iyaye.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga shirrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. (Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammad (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka : ‘Yan uwana musulmi a yau zamu tattauna ne akan wani al’amari mai girma, haqqi ne da Allah ya haxa haqqinsa da shi a wurare da dama a cikin Alqur’ani mai girma, kuma babu tsira ko rabauta ga wanda duk ya tozarta wannan haqqi, wannan haqqi kuwa shi ne haqqin iyaye.

Haqqin iyaye a musulunci, haqqi ne mai girma, saboda haka ma Allah Maxaukakin Sarki ya haxa shi da haqqinsa a wurare da dama a cikin alqur’ani mai girma, kamar faxin Allah :

(وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَبِذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ36) [النساء: ٣٦].

Ma’ana : (Ku bauta wa Allah kada ku yi shirka da shi da wani abu, sannan ku kyautata wa iyaye da makusanta da marayu da Miskinai) (Annisa’i: 36).

Da faxinsa :

(وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا23) [الإسراء : ٢٣].

Ma’ana : “Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai shi kaxai, kuma a kyautata wa iyaye) (Al- Isra’i : 23).

An karvo daga Abdullahi xan Mas’ud – Allah ya yarda da shi – ya ce, na tambayi Manzon Allah (ﷺ) na ce, “wane aiki ne Allah ya fi so?” sai ya ce, “Sallah akan lokacinta” sai na ce, “Sannan me?” sai ya ce, “Bin iyaye” sai na ce, “Sannan me?” sai ya ce, “Jihadi a kan tafarkin Allah”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

An sake karvo wa daga gare shi – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye”. Tirmizi da Ibnu Hibban suka rawaito.

Waxannan ayoyi da hadisai suna tabbatar mana da wajabcin bin iyaye da kyautata musu.

Ya uwana musulmi : Haqqin iyaye yana dauwama ko da iyayen sun mutu, kamar yadda yake ba ya saraya koda iyayen kafirai ne, wajibi ne xa ya yi musu biyayya da abu mai kyau, wanda ba savon Allah ba. Allah Maxaukakin Sarki ya ce :

(وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ وَهْنًا عَلَى وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ إِلَيَّ الْمَصِيرُ14 وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلى أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا وَاتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ15) [لقمان: ١٤ – ١٥].

Ma’ana : “Mun yi wa mutum wasiyya da iyayensa, mahaifiyarsa ta xauke shi rauni akan rauni, xaukan cikinsa da yaye shi shekaru biyu, ka gode min da iyayenka, gareni makoma take. Idan suka tilastaka a kan ka yi shirka da ni cikin abin da baka ilimi a kai, kada ka bi su, ka zauna da su a duniya da kyakkyawa, ka bi hanyar wanda ya mayar da lamarinsa gareni, gareni makomarku take, sai in baku labarin abin da kuke aikatawa”. (Luqman : 14).

Sannan an karvo daga Asma’u ‘yar Abubakar – Allah ya qara mata yarda – ta ce, mahaifiyata ta zo wajena ziyara a lokacin tana arniya bata musulunta ba, sai na tambayi Annabi (ﷺ) na ce masa : “Mahaifiyata ta zo wajena tana son (ganina) ko (ya halatta) in sada zumuncinta?” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Eh, ki sada zumuncinta” (ma’ana ki tarbeta, ki ba ta masauki). Bukhari ne ya rawaito.

Bin iyaye da kyautata musu yana daga cikin manya – manyan ayyukan da suke kusantar da mutum ga Allah Maxaukakin Sarki, kuma dalili ne da yake sa Allah ya yaye wa mutum musiba da bala’i, kamar yadda labarin mutanen nan guda uku da suka shiga kogo dutse ya rufe su take nuna wa, yayin da suka cewa junansu “kowa ya yi kamun qafa a wurin Allah da wani aiki na alheri da ya yi, ko Allah ya fitar da mu daga cikin wannan musiba” nan da nan xayansu ya yi kamun qafa a wurin Allah da barin wani aikin savo da ya yi, sai dutsen ya xan buxe kaxan. Na biyun ma ya yi kamun qafa da kiyaye amana da ya yi, sai dutsen ya qara buxe wa kaxan. Na ukun shi kuma ya yi kamun qafa da bin iyayensa da yake yi, ya ce, “Ya Allah!, haqiqa ni na kasasance ina tare da iyayena tsofaffi guda biyu, da mata ta da ‘ya ‘yana, ina yi wa iyayena kiwon dabbobi, idan na tafi kiwo na tatso nonon dabbobin nan, ina fara bawa iyayena su sha, sannan in bawa iyalina, sai wata rana na yi nisa wurin kiwo, ban dawo ba sai da yamma, na sami iyayen nan nawa sun yi barci, na tatsi nonon nan kamar yadda na saba, na zo da shi, na tsaya a kansu ina jiran su farka in fara ba su, domin ba na son in tashe su daga barcin da suke yi, kuma ba na son in fara bawa ‘ya ‘yana kafin in ba su. Haka na tsaya ina jiransu’ ‘ya’yana suna ta kuka a kusa da ni, amma ban ba su ba, har sai da asuba ta yi, iyayena suka farka na fara ba su, sannan na bawa ‘ya’yana. Ya Allah idan na yi wannan don neman yardarka ka buxe mana qofa, sai Allah ya buxe musu qofa har suka riqa ganin sama,suka fito suka ci gaba da tafiya”.

A wannan hadisi mai girma za mu ga yadda wannan bawan Allah ya yi kamun qafa da bin iyayensa, kuma Allah ya yaye masa halin qunci da yake ciki.

Ya ‘yan uwana musulmi : Yana daga cikin haqqin iyaye a kan xansu ya sassauta musu magana, ya yi musu magana mai daxi, ya ciyar dasu, ya tufartar dasu idan faqirai ne, saboda Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

(إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا23وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُلْ رَبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا24) [الإسراء: ٢٣ - 24].

Ma’ana : “Idan xayansu ko kuma su duka biyun suka tsufa tare da kai, to kada ka ce musu tir, kada ka yi musu tsawa, ka faxa musu magana mai girma (mai daxi). Ka sassauta musu fika – fikan rahama, ka ce ya Ubangiji ka yi musu rahama kamar yadda suka rene ni ina qarami”. (Al – Isra’i : 23 – 24).

Hakanan yana daga cikin haqqinsu ya sada zumuncinsu da zumuncin abokansu, domin ya inganta cewa Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – yana da jaki da yake hawa idan ya gaji da hawan raqumi, kuma yana da wani rawani da yake xaure kansa da shi. Wata rana yana tafiya akan wannan jakin a cikin garin Makkah, sai wani mutumin qauye ya wuce ta kusa da shi, sai Abdullahi xan Umar ya cewa mutumin qauyen nan, “Ashe ba kai ne wane xan wane ba?” ya ce, “Ni ne” sai Abdullahi xan Umar ya bashi jakin nan ya ce, “hau, ga kuma rawani ka sanya a kanka”. Sai wasu daga cikin Abokan Abdullahi xan Umar suka ce, “Allah gafarta malam, mun ga ka baiwa wannan mutumin qauyen jakinka da kake hutawa a kansa, da rawaninka da kake xaure kanka da shi, ya ya haka?”. Sai ya ce musu : “Saboda ni na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Yana cikin mafi kyan aikin alherin mutum ya sada zumuncin waxanda mahaifinsa yake son su bayan ya mutu. To baban wannan mutumin qauyen abokin Umar ne (mahaifina). Muslim ne ya rawaito wannan hadisi.

Allahu Akbar!. ‘Yan uwa ku duba ku ga yadda Abdullahi xan Umar ya girmama xan abokin mahaifinsa, saboda waccan hadisi da ya ji a wajen Manzon Allah (ﷺ) to a yau me waxanda suke cin mutuncin iyayensu za su faxa wa Allah a gobe qiyama!, idan ya zamana xan abokin mahaifinka ka girmama shi, ina ga Abokin mahaifinka, to kuma ina ga mahaifanka!!.

‘Ya ‘yan uwana musulmi : Magabatanmu na qwarai sun buga kyawawan misalai a wajen bin iyayensu.

Muhammad xan Sireen – Allah ya yi masa rahama – ya kasance idan mahaifiyarsa tana magana sai ya qasqantar da kansa ya yi shiru.

Ibnu Auf – Allah ya yi masa rahama – ya ce, : Wani mutum ya shigo wajen Muhammad xan sireen a lokacin yana gaban mahaifiyarsa, sai wannan mutumin ya ce, “me ya sami Muhammad ne, ko bai da lafiya ne?” sai suka ce masa : “a’a, haka yake idan yana gaban mahifiyarsa”.

Aliyu xan Aliyu xan Husain jikan Manzon Allah (ﷺ) – Allah ya yi masa rahama – yana xaya daga cikin manya – manyan tabi’ai, ya kasance mai tsananin biyayya ga mahaifiyarsa, har wata rana aka ce da shi, “kana tsananin bin mahaifiyarka, har ma mun ga ba ka iya cin abinci tare da ita a kwano xaya”, sai ya ce musu : “ina tsoron kada in kai hannuna kan wani abin da ta yi sha’awa a abincin, in zama na sava mata”.

Hakanan Imam Haywa xan Shuraih – xaya daga cikin manya – manyan malaman tabi’ai – ya kasance idan yana zaune yana bada karatu, mahaifiyarsa ta kira shi, ta ce ya je ya ba kaji abinci, sai ya tashi da gaggawa ya bar almajiransa a zaune.

Waxannan kaxan kenan daga cikin misalan yadda magabata na qwarai suke bin iyayensu, to a yau me yasa matasanmu suke sakaci da bin iyayensu, har ka samu a cikinsu wanda yake savawa iyayensa saboda kawai ya samu yardar abokinsa!,

Saboda haka ina muku wasiyya – yaku yara – da ku yi wa iyayenku wasiyya, ku yi qoqarin samun yardarsu da sanya musu farin ciki duniya da lahira, ka sani ya kai xan uwa me mahifinka yake buqata a wajenka fiye da ka tsaya kusa da shi yayin da yake buqatar hakan, ka taimake shi a lokacin da yake son taimakon, ba fa wani abu da mahaifiyaka take so a wajenka fiye da kalmar tausaya wa, da magana mai daxi da so da girmamawa. Allah mai girma da buwaya yana cewa :

(وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا 23وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُلْ رَبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا24) [الإسراء: ٢٣ - ٢٤ ].

Ma’ana : “Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai shi kaxai, kuma a kyautata wa iyaye. Idan xayansu ko kuma su duka biyun suka tsufa tare da kai, to kada ka ce musu tir, kada ka yi musu tsawa, ka faxa musu magana mai girma (mai daxi). Ka sassauta musu fika – fikan rahama, ka ce ya Ubangiji ka yi musu rahama kamar yadda suka rene ni ina qarami”. (Al – Isra’i : 23 – 24).

Allah ya yi mana albarka cikin abin da muka ji, na alqur’ani da hadisi, haqiqa Allah mai iko ne akan dukkan komai.

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan qarshe yana ga masu tsoron Allah, Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (ﷺ) da iyalansa da Sahabbansa da waxanda suka bi su gaba xayansu, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Yaku ‘yan uwana musulmi : Sava wa iyaye yana daga cikin manya – manyan zunubai, waxanda suke jefa mutum cikin wutar Jahannama.

An karvo daga Abu Bakrata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Ba na baku labarin mafi girman zunubai ba? Ya faxi haka har sau uku. Sai muka ce “Bamu labari ya Rasulallahi” Sai Manzon Allah ya ce, “Shirka da Allah, savawa iyaye..” Bukhari da Muslim.

Hakanan An karvo daga Abdulallahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Mutane uku Allah ba zai kalle su ba ranar alqiyama, Mai sava wa iyayensa, da mai dauwama akan shan giya, da mai gori”. Nasa’i ne ya rawaito shi.

Yana daga cikin haxarin savawa iyaye Allah Maxaukakin Sarki yana gaggauta azabarsa tun a nan duniya kafin lahira, Manzon Allah (ﷺ) yana cewa : “Babu wani zunubi da ya cancanta Allah ya gaggauta wa mai yinsa uquba a duniya, haxe da abin da aka tanadar masa na azaba a lahira, irin qetare iyaka (zaluntar wani) da sava wa iyaye” Imamu Ahmad ne ya rawaito.

Yana cikin savawa iyaye xaga murya sama da ta su, da yanke musu magana idan suna yi, da yi musu tsawa, da tilasta su a kan wani abin da basu yi niyya ba, da yi musu mummunan kallo na wulaqanci, kamar yana kallon maqiyinsa da xaya daga cikin 'ya'yansa da yake yi wa tsawa.

Yana cikin sava wa iyaye jinkirta biya musu buqata, da ja musu rai har su gaji da tambaya su haqura. Allah yana cewa :

(فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا23) [الإسراء: 23]

Ma’ana : “ Kada ka ce musu tir, kada ka yi musu tsawa, ka faxa musu magana mai girma (mai daxi).”

Ku ji tsoron Allah – Yaku bayin Allah – ku kiyayi savawa iyaye, ku guji gabatar da wasu akan iyaye, saboda babu wani zunubi da Allah yake gaggauta azabarsa kamar savawa iyaye, kuma abin da mutum ya yi shi za a yi masa.

An samu wani mutum da ya xauki babansa tsoho ya tafi da shi can cikin sahara, cikin daji, sai uban ya ce wa xan “Ya kai xana ina zaka da ni ne? sai xan ya ce, “Ai na gaji da zama da kai ne” sai uban ya ce, “to me zaka yi min yanzu?” sai ya ce, “Ina so in yanka ka ne!!?” sai uban nan ya ce wa xansa “idan kuwa haka ne, to matsa da ni wajen wanncan dutsen?” sai xan ya ce, “A! saboda me?” sai uban ya ce, “Saboda ni ma a can na kashe nawa mahaifin a wajen wancan dutsen, don haka nima ka kashe ni a can, kuma kai ma zaka samu cikin ‘ya ‘yanka wanda zai kashe ka a nan!!”. Haka sakamako yake irin abin da aka aikata.

Don haka wajibi ne a kanmu – Musulmi – mu yi wa iyayenmu biyayya kamar yadda Allah ya yi umarni, mu kyautata musu daidai gwargwadon ikonmu, da haka ne zamu samu rabauta a duniya da lahira.

Tags: