islamkingdomfacebook islamkingdomyoutube islamkingdomtwitte


Zakka, Hikimominta Da Hukunce-hukuncenta


9390
Surantawa
Haqiqa yana daga hikimar Ubangiji mai girma, cewa ya sassa'ba tsakanin bayinsa a cikin halayensu da arziqinsu, haqiqa Ubangijinku Mai hikima ne Masani. Sai ya yalwatawa sashinsu arziqi, ya sanya sashi koma bayan haka.haqiqa Allah Mabuwayi, ya wajabta wa mawadaci haqqi da zai ba wa talakawa, sanna haqqi ga roqo da ma wanda ba ya roqo. Allah ya wajabta wani haqqi a dukiyar mawadata, da za su ba wa ‘yan’uwansu talakawa, don su tallafe su da shi, kuma ya sanya wannan rukuni ne daga rukunan musulunci,

Manufofin huxubar

Bayanin hukuncin zakka da matsayinta a Musulunci.

Bayanin abin da wannan shari’a ta qunsa na hikimomi masu qayatarwa.

Bayanin hukunce-hukuncen da suka rataya da nau’o’in dukiyoyin da ake fitar da zakka.

Bayanin guraren da ake sarrafar da zakka, da kirdado wajen karvar ta da rabar da ita.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah, haqiqa yana daga hikimar Ubangiji mai girma, cewa ya sassava tsakanin bayinsa a cikin halayensu da arziqinsu, haqiqa Ubangijinku Mai hikima ne Masani. Sai ya yalwatawa sashinsu arziqi, ya sanya sashi koma bayan haka. Kuma shi ne mai hikima Masani.

( قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَنْ يَشَاءُ وَيَقْدِرُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ36 ) [سبأ: 36]

“Ka ce, haqiqa Ubangiji yana yalwata arziqi, ga wanda ya so, kuma yana quntatawa (ga wanda ya so), sai dai da yawan mutane ba su sani ba.”

Ya jarrabi wasu da dukiya, sai ya yalwata musu ita, Ya ba su dangogin dukiya. Ya jarrabi wasu da talauci. Allah ya ce,

( فَأَمَّا الْإِنْسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ 15 وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ 16 كَلَّا بَل لَا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ 17 ) [الفجر: 17]

“Amma mutum idan Ubangijinsa ya jarrabe shi, sai ya girmama shi, ya yi masa ni’ima, sai ya ce, Ubangijina ya girmama ni. Amma idan ya jarrabe shi sai ya quntata masa arziqinsa sai ya ce, Ubangijina ya tozarta ni. A’a, ba haka lamarin yake ba…).

Ai ba duk wanda Allah ya yalwatawa ba hakan yake nuna ya fi sonsa. Kuma ba duk wanda aka quntatawa ba, hakan yana nufin ba ya son sa, sai dai ita duniya ce, Allah yana ba da ita ga wanda ya ga dama, kuma ya hana wasu daga cikin bayinsa, kuma Yana da ilimi da hikima a cikin hakan.

Ya jarrabi talakawa da mawadata, ya jarrabi mawadaci da dukiya, domin ya ga shin wannan dukiyar za ta zama dalilin godewarsa, ga ni’imomin Ubangiji, da tsayuwa da haqqinsa? Kuma ya jarrabi talaka don ya ga shin zai zama daga masu haquri masu yarda, ko kuwa zai kasance daga cikin masu fushi?

ya dasa son dukiya a cikin zukata, Allah ya ce,

وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا20) [الفجر: 20] (

(Kuma kuna son dukiya so mai yawa).

Ita wannan dukiya ni’ima ce ga wasu mutane, kuma musiba ce ga wasu. Ni’ima ce ga wanda ya karve ta da haqqinta, kuma kashe ta inda ya kamata, ya san cewa Allah yana da haqqi a cikin wannan dukiyar, ya ba da wannan haqqin cikakkiyar. Wannan, dukiya ta zama ita ce dalilin nagarta da daidaituwar halisa, da rigegeniyarsa a cikin aiki na gari. Wasu kuwa dukiya ta zamo musu dalilin tsaurin kai, da taqama da fankama, da ruxuwa da kawunansu. Sai suka hana haqqoqin Allah da ya wajaba a cikin dukiyarsu. Sai ba su ba da haqqin dukiyar ba, sai ma dukiyar ta zamo sababin azabtar da su.

( وَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَأَوْلَادُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُعَذِّبَهُمْ بِهَا فِي الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنْفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ 85 ) [التوبة: 85]

(Kada dukiyarsu ta qayatar da kai, ko ‘ya’yansu, kaxai Allah yana nufin ya azabtar da su da ita a rayuwr duniya, kuma rayukansu su fita alhali suna kafirai).

Savanin wanda ya ruxu da kansa, ya ce:

( قَالَ إِنَّمَا أُوتِيتُهُ عَلَى عِلْمٍ عِنْدِي ) [القصص: 78].

(Ya ce, kawai an ba ni ita ne saboda wani sani da nake da shi).

Ya kai musulmi, haqiqa Allah Mabuwayi, ya wajabta wa mawadaci haqqi da zai ba wa talakawa, sanna haqqi ga roqo da ma wanda ba ya roqo. Allah ya wajabta wani haqqi a dukiyar mawadata, da za su ba wa ‘yan’uwansu talakawa, don su tallafe su da shi, kuma ya sanya wannan rukuni ne daga rukunan musulunci, domin zakka ita ce rukuni na uku daga rukuna musulunci da aka gina shi a kansu. “An gina musulunci a kan abubuwan biyar: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya bisa cancanta sai Allah, kuma cewa, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsayar da salla, da ba da zakka, da azumin watan Ramadana, da Hajjin xakin Allah.” Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi, daga Abdullah xan Umar, Allah Ya qara yarda a gare shi.

A cikin littattafai Bukhari da Muslim, daga xan Abbas, Allah ya yarda da su, faxin Manzon Allah (ﷺ), ga Mu’azu xan Jabal, “Ka sanar da su cewa Allah ya wajabta musu sadaka da za a karva daga mawadatansu a ba wa talakawansu.

Nassoshin Alqur’ani da sunna sun tabbatar da kasancewar zakka rukuni ce na Musulunci, da kuma bayanin muhimmancinta. Allah Ta’ala ya ce:

( وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ 5 ) [البينة: 5]

“Ba a umarce su ba face su bautawa Allah, suna masu tsarkake addini a gare shi, suna masu bin miqaqqen addini, kuma su tsai da sallah su ba da zakka. Wannan shi ne addinin hanya miqaqqiya.”

Ya kai musulmi, haqiqa, zakka jarraba ce da gwaji wadda Allah kan jarrabi mawadata da ita. Mai gaskiya a imaninsa zai kuvuta daga wannan jarrabawa, ta hanyar fitar da zakka a cikin daxin rai. Yana mai sakankancewa da wajabcinta, yana mai qudurce haka, yana ba da ita domin biyayya ga Allah da godewa falalarsa da ni’imominsa. Allah Ta’ala ya ce:

( خُذْ مِنْ أَمْوَالِهِمْ صَدَقَةً تُطَهِّرُهُمْ وَتُزَكِّيهِمْ بِهَا وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إِنَّ صَلَاتَكَ سَكَنٌ لَهُمْ وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ 103 ) [التوبة: 103]

(Ka karvi zakka daga dukiyoyinsu wadda za ka tsarkake su, ka tsaftace su da ita, kuma ka yi addu’a a gare su, haqiqa addu’arka nutsuwa ce a gare su, kuma Allah Mai ji ne, Masani).

Allah yana umartar Annabinsa Muhammadu da karvar zakka daga dukiyoyin mawadata, “Ka karvi zakka daga dukiyoyinsu.” Allah Ta’ala Ya bayyana hikimarsa ta wajabatata, da faxinSa: “Da za ka tsarkake su, ka tsaftace su da ita.”

Don haka ke nan zakka tsarki ne ga mai yinta. Tana tsarkake zuciyarsa daga cutar qwauro da rowa, tana sanya shi ya yi kyauta ya yi alheri. Kuma tana tsaftace dukiya daga dauxarta da qazantarta. Domin dukiyar da ba a fitar da zakkarta ba, takan kwashi dauxa da qazanta, kuma babu abin da zai tsaftace ta sai zakka. Kuma ita zakka tsarki ce ga zuciya, domin tana qarfafa iman. Domin mai fitr da ita yana rinjayar fizge-fizgen son rai da sha’awoyin zuciya da wasi-wasin shaixan. Ya fitar da ita ne don biyayya ga Allah yana mai turmusa hancin maqiyin Allah. Allah ya ce,

الشَّيْطَانُ يَعِدُكُمُ الْفَقْرَ وَيَأْمُرُكُمْ بِالْفَحْشَاءِ وَاللَّهُ يَعِدُكُمْ مَغْفِرَةً مِنْهُ وَفَضْلًا وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ [البقرة: 268]

(Shaixan yana yi muku alqawarin talauci, kuma yana umartar ku da alfasha, Allah kuwa yana yi muku alqawarin gafara daga gare shi, da falala, kuma Allah Mai yalwar falala ne, Masani).

Kuma zakka tana havaka dukiya, domin dukiyar da aka fitarwa zakka tana havaka, kuma Allah yana saukar da albarka a cikinta. Ya zo a cikin Sahihu Muslim daga Abu Huraira, Annabi (ﷺ) ya ce, “Babu wata dukiya da za ta tawaya saboda fita da zakka.”

Ya kai xan’uwana musulmi, ka ba da zakkar dukiyarka kana mai sakin zuciyarka. Ka ba da zakkar dukiyarka, kana mai qudurce wajabcinta a musulunci. Ka ba da zakkar dukiyarka domin biyayya ga Allah da Manzonsa. Ka ba da zakkar dukiyarka don dukiyarka ta wanzu a gare ka, albarkarta ta qaru, alherinta ya yawaita, bala’i ya yaye daga gare ka.

Ya xan’uwana Musulmi! Ka dubi ni’imar da Allah ya yi maka na wannan dukiya ba ka same ta ba don qarfin jikinka, ko basirar ra’ayinka. Tsantsar falala ce, kawai ta Allah da karamcinsa, da baiwarsa da kyautatawarsa a gare ka. Dubi wannan dukiya, sanna ka dubi zakkarta, za ka ga zakkar rubu’in ushurinta ne (Rabin rabin xaya bisa goma ne) ko a ce, biyu da rabi a cikin xari (2.5%). Ya ba ka da yawa, amma ya gamsu da kaxan daga wajenka. Sannan wannan xan kaxan xin ma amfaninsa kanka zai dawo duniya da lahira.

Ya kai Musulmi! Ka yi kwaxayi a bisa fitar da zakka, ka yi kwaxayi a bisa qididdige dukiya, ka tantance wajen lissafin, ka lissafe ta a duniya kafin a lissafa maka ita a lahira.

( يَوْمَ لَا يَنْفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ 88 إِلَّا مَنْ أَتَى اللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ 89 ) [الشعراء:88 - 89]

“Ranar da dukiya da ‘ya’ya ba za su yi amfani ba, sai wanda ya zo wa Allah da zuciya lafiyayyiya.”

Ya kai xan’uwana Musulmi, ka fitar da zakka da niyya da nufi mai kyau, domin Allah, don ayyukanka sun ta’allaqa ne a bisa niyya. Dole ne sai an yi niyya a yayin fitarwar. Niyyar ba da wannan wajibi mai girma. Idan ka fitar da ita to ka yi bushara da alheri da albarka daga Allah, da lada mai girma a ranar gamuwa da Ubangijinka.

Ya kai Musulmi, haqiqa Allah Mai girma da xaukaka ya wajabta zakka a dangogin dukiyoyi. Ya wajabta zakka da farko a dangogin abubuwan da kan fito daga qasa, na hatsi da kayan marmari, Allah ya ce,

( وَآَتُوا حَقَّهُ يَوْمَ حَصَادِهِ ) [الأنعام: 141]

(Kuma ku ba da haqqinsa a ranar girbinsa).

Da faxinsa:

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا أَنْفِقُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا كَسَبْتُمْ وَمِمَّا أَخْرَجْنَا لَكُمْ مِنَ الْأَرْضِ وَلَا تَيَمَّمُوا الْخَبِيثَ مِنْهُ تُنْفِقُونَ ) [البقرة: 267]

(Ya ku waxanda suka yi imani ku ciyar daga daxaxan abin da kuka tsururuta, daga kuma abin da muka fitar muku daga qasa. Kada ku nufi lalatacce a cikinsa kuna ciyarwa).

Ya sanya sharaxin wannan hatsi ya kai wusuqi biyar, wato abin da ya yi daidai da kilo xari tara. (900kg). ya wajabta usuhuri a cikinsa (Xaya bisa goma) na hatsi da kayan marmari, idan ba a wahala a wajen shayar da ita shukar ba, (wato kamar shukar damina). Kuma ya sanya rabin Ushurinta (xaya bisa ashirin), idan an shayar da ita da wahala (kamar ta hanyar amfani da ban-ruwa). Kuma shi Maxaukakin Sarki bai wajabta zakka a kayan lambu da kayan marmari ba. Saboda su ba a ajiyar su, su abincin lokacinsu ne, savanin hatsi da ‘ya’yan itatuwa wanda ake aunawa kuma ake ajiyarsu domin su sukan daxe tsawon shekara.

Ya kai musulmi, haka nan Allah Ya wajabta ta a dabbobin ni’ima kamar raquma da shanu, da awaki, idan su masu fita kiwo ne. Suna kiwo a mafi yawancin lokacin shekara ta hanyar cin ciyayi, ba a kawo musu ciyawa da ruwa, an tandar masu komai. To idan haka dabba take, zakka ta wajaba a cikinta. Mafi qarancin nisabin raquma, shi ne biyar. Nisabin awaki da tumaki arba’in. Nisabin shanu, kuwa talatin.

Ita kuwa dabbar da ake kawo mata ciyawa da ruwa a mafi yawan lokutan shekara babu zakka a cikinta. Sai dai idan mai ita yana tanadinta ne don kasuwanci. Ma’ana, ta zama wata haja ce ta kasuwanci, wannan ana yi mata qima duk shekara, a fitar da zakkarta rubu’in Ushurinta. Su kuwa dabbobin gonaki waxanda ba kasuwanci aka yi da su ba, kuma ba fita kiwo suke yi ba, sai dai masu su ne suke ci da su. Don su riqa cin namansu, su riqa shan nononsu, to babu zakka a cikinsu.

Allah Ya wajaba zakka a cikin kadarorin kasuwanci. Kadarorin kasuwanci kuwa su ne duk abin da musulmi ya tanada don saye da sayarwa na hajoji daban daban. Kamar abinci, ko tufafi, ko abin hawa da makamantansu, to za mu yi masa qima a wata fitar da zakka, mu fitar da rubu’in Ushurinsa, na farashinsa, abinci ne ko tufafi ko kayan kwanuka ko motoci, ko safaya fat, ko filaye duk waxannan suna shiga cikin kadarori. Za mu yi masa farashi a qarshen shekara, sai a duba farashin abu a yanzu, farashin ya qaru ko ya ragu. Da musulmi zai sai filotin qasa don kasuwanci, sai filotin ya shekara, za a yi masa farashi a qarshen kowace shekara, a kalli, farashinsa na yanzu, ya biya rubu’in Ushurin farashin da aka yi masa. Da a ce farashin sayen wajen, zai zama, filoti xaya dubu xari, amma a qarshen shekara, ya zama naira dubu xari biyar, to za mu ce, zakkarsa za ta kama a kan dubu xari biyar. Za a fitar da rubu’in Ushurin farashinsa. Da kuma a ce, farashin, zai faxi zuwa dubu hamsin, to za mu ce zakkar tana kan naira dubu hamsin xin, in hakan ya kai nisabi, haka Allah ya shar’anta.

Zinare da azurfa, Allah ya wajabta zakka a cikinsu, domin su ne ma’aunin dukiya. Allah Ta’ala ya ce:

( وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالْفِضَّةَ وَلَا يُنْفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ 34 يَوْمَ يُحْمَى عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَى بِهَا جِبَاهُهُمْ وَجُنُوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ هَذَا مَا كَنَزْتُمْ لِأَنْفُسِكُمْ فَذُوقُوا مَا كُنْتُمْ تَكْنِزُونَ 35 ) [التوبة:34 - 35]

)Waxannan da suke taskance zinare da azurfa, kuma ba sa ciyar da ita a cikin tafarkin Allah, ka yi musu bushara da azaba mai raxaxi. Ranar da za a yi msu lalas da ita a wutar Jahannama, sai a qona goshinansu da gefunansu da bayansu da ita, a ce, wannan shi ne abin da kuka taskake ga kawunanku, to xanxani abin da kuka kasance kuna taskakewa).

Don haka dai ana fitar da zakkar kuxaxe guda biyu, zinare da azurfa, da takardun kuxi da suke matsayinsu, kuma suka xau hukuncinsu wajen ciniki da ma’amala. Ana fitar da rubu’in Ushurinta.

Ya kai musulmi, hannayen jari, a kamfanoni mabambanta sun kasu kashi biyu. Akwai hannayen jari da ake kasuwancinsu, wanda musulmi yake neman riba da su. Yake fitar da su, don sayarwa a lokacin da ake nemansu, ya voye yayin da ba a buqata. Wannan ana zakkarsu a qarshen kowace shekara, za a fitar da qimarsu ta lokacin, domin suna matsayin kuxin da ke hannunka ne.

Su kuwa hannayen jari da aka sanya su kamar ajiya ce, ba a sai da su, ko a saya, sai dai a amfana daga ribarsu, to idan aka karvi ribarsu ta shekara sai ka fitar da zakkarsu, idan kuwa ki cinye ribar to babu zakka su a cikinsu.

Su kuwa gidaje da filaye wanda ake hayarsu zakka tana wajaba ne a cikinsu, kawai daga sanda ake qulla yarjejeniyar hayar idan ka karvi kuxin haya a qarshen shekara to ka ba da zakkar ta. In kuwa kana karva duk wata shida ne, ka kashe b ka ajiyewa, to babu zakka a cikinta. Amma idan kana karvar ta a qarshen shekara ne, ko kana karva ka ajiye, to za ka ba da zakkarta. In kuwa kaxan-kaxan kake karva ka cinye to babu zakka a kai.

Gidanka da kake zaune a cikinsa, da motarka da kake shiga, duk wannan ba zakka a cikinsu. Domin Annabi (ﷺ) yana cewa: “Babu zakka a kan Musulmi a cikin bawansa da dokinsa.” Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi daga Abu Huraira.

'Yan uwa musulmi, wannan shi ne abin da za faxa, ina nemawa kaina da ku da sauran musulmi gafarar Allah, ku nemi gafararsa, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai.

Yabo daddaxa mai albarka ya tabbata ga Allah, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma ya yarda da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Yabo na shi ne a duniya da lahira. Kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu, bawansa ne, kuma Manzonsa ne, ya aiko shi da rahama da shiriya. Allah ya yi tsira da aminci da albarka a gare shi, da alayensa zavavvu da sahabbansa masu girma da tabi’ai, da waxanda suka bi su da kyautatawa, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka: Ya ku musulmai, haqiqa zakka farilla ce, kamar yadda Allah Ya ambata a cikin littafinsa ya ce:

(إِنَّمَا الصَّدَقَاتُ لِلْفُقَرَاءِ وَالْمَسَاكِينِ وَالْعَامِلِينَ عَلَيْهَا وَالْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِي الرِّقَابِ وَالْغَارِمِينَ وَفِي سَبِيلِ اللَّهِ وَاِبْنِ السَّبِيلِ فَرِيضَةً مِنَ اللَّهِ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ 60) [التوبة: 60]

(Haqiqa zakka haqqi ne na mabuqata, da miskinai, da masu aiki a kanta, da waxanda ake son karkato da zuciyarsu (ga musulunci) da wajen fansar bayi, da waxanda ake bi bashi, da wajen xaukaka kalmar Allah, da xan tafarki. Farilla ce daga Allah, kuma Allah ya tabbata masani, Mai hikima).

Allah bai xora rabon zakka a kan wani Annabi ko mala’ika ba, a’a, Shi ya jivinci raba ta da kansa.

Ya ku musulmai! Ku ji tsoron Allah a cikin zakkarku. Ya kai musulmi! Ka sani kai abin amincewa ne a kanta. Don haka ka isar da amana zuwa ga waxanda suka cancanta:

( إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَنْ تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَى أَهْلِهَا ) [النساء: 58]

(Haqiqa Allah yana umartar ku da ku mayar da amana zuwa ga masu ita).”

Faqirai da miskinai waxanda ba su da komai, ko suke da abin da ya gaza wadatar da su buqatunsu na lalura. Ba su da wani tsayayyen albashi ko wata kadara mai kawo musu abin masarufi ko tsayayyar sana’a, ko wani ya xauki nauyin ciyar da su. Sai a ba su abin da zai ishe su shekar guda daga zakka. A ba faqiri da miskini gwargwadon abin da zai ishe shi. A taimakawa mai neman aure game da aurensa. Domin wannan yana cikin muhimman buqatu. A ba wa faqiri da miskini abin da zai ishe su, wannan idan zatonka ya rinjaya a kan shi ya fi cancantarta. Idan kuwa ka ga alamomin wadata a jikinsa, ko alamomin qarfi da karsashi, to ka yi masa nasiha, ka yi masa gargaxi, domin wasu mutane sun zo wa Annabi (ﷺ) suna tambayarsa, ya ba su zakka, sai ya dube su, sai ya gan su qarfafa. Sai ya ce, “In kuna so in ba ku, amma ku sani babu haqqi a cikin zakka ga mawadaci, ko qaqqarfa da zai iya nema.” Ahmad da Abu Dawud da Nasa’i ne suka rawaito daga Ubaidullah xan Addiy.

Ya kai Musulmi! Ka ba wanda ake bi bashi zakka. Wato wanda ya ci bashi don maslahar kansa, ko don maslahar wani, wato ya xau bashi, amma ya gaza biya, da sharaxin ba zai ci gaba da irin wannan sakacin ba. Ka ba wa wanda ya ci bashi don maslahar al’umma ko da mawadaci ne, ka ‘yanta wuyan fursunoni na musulmi, ka taimaki mai jihadi, da wanda guzurinsa ya qare, wannan ita ce shari’ar Ubangijin talikai.

Ya kai musulmi! Idan ka zama mawadaci, to kar ka karvi zakka. Idan kuwa ka karva, bayan Allah ya wadata ka ga barin karvar, to ka sani kana cin mafi munin haramun ne. Ya zo a Bukhari da Muslim daga Ibn Umar, Annabi (ﷺ) ya ce, “Roqo ba zai qyale xayansu ba, har sai ya gamu da Allah babu ko tsokar nama a fuskarsa.” A cikin Sahihi Muslim kuma daga hadisin Abu Huraira, Manzo Allah (ﷺ) ya ce, “Wanda ya roqi mutane don tara dukiya, to yana roqar garwashin wuta ne, in ya so ya roqa kaxan, ko ya roqa da yawa.” A cikin Musnad na Imam Ahmad, daga Abi Huraira, Manzo Allah (ﷺ) ya ce, “Bawa ba zai buxe wa kansa qofar roqo ba, sai Allah ya buxe masa qofar talauci”. Haka kuma a cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Abu Huraira, ya ce, Manzo Allah (ﷺ) ya ce, “Ita wadata ba wai yawan kadarori ba ce, wadata ita ce wadatar zuci.”

Ya kai Musulmi! Bukhar da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Huraira, ya ce, Manzo Allah (ﷺ) ya ce, “Miskini ba shi ne wanda yake yawo cikin mutane, loma xaya ko biyu take dakatar da shi ba, ko dabino xa ko biyu. Sai dai cikakken miskini, shi ne wanda, ba shi da abin da zai wadatar da shi, kuma ba a faxakuwa da shi ballantana a ba shi sadaka, kuma ba ya tashi ya roqi mutane”

Ya kai xan’uwana Musulmi! Da yawa waxanda ba su cancanci zakka ba suna roqo a ba su. Kuma su nace wajen nema, alhali Allah ya ba su qarfin jiki, da lafiyarsa, da ikon yin aiki. Sai dai su sun saba da hakan ne. Suka ga cewa al’ada duk shekara sai an ba su. Da yawa wasu mutane suna roqon zakka waxanda da farko su talakawa ne, sai Allah ya wadata su, ya ba su yaran da za su tallafa musu, a bisa lamuransu. Sai dai mutuwar zuciya da cutar kwaxayi, sun sanya su suna roqonta alhali su mawadata ne ga barinta.

Ya xan’uwa, ka kirdadi, waxada ba sa roqo, ka bibiyi masu iyali (masu kamewa), waxanda ba sa nacewa da roqon mutane. Wanda bai sani ba zai xauka su mawadata ne. Saboda kame kai. Ka yi kirdadon wanda yake bayyana matsayin mawadaci, alhali kuwa Allah ya san halin da yake ciki. Ka kirdadi wanda basussuka suka yi masa yawa.

Lalle abu ne muhimmi, mu san cewa, Allah ya sanya zakka hanya ce, ta haxin kan al’umma da dunqulewarta, da jinqan sashi ga sashi. “Ku jiqan wanda ke qasa, wanda ke sama sai ya jiqan ku”, “Masu jinqai, Mai rahama zai jinqan su.” Ahmad da Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito.

Da mawadata za su ba da zakkar dukiyoyinsu, da matalauta sun wadatu. Sun kare mutuncinsu, kuma an samu sauqin aikata.

Ya ku bayin Allah! Ku yi kwaxayi a bisa zakkar dukiyarku, ku sadar da ita ga waxanda suka cancanceta. Ku boye ta, idan kuka san cewa wanda zai karve ta mai kame kai ne ba ya so lamarinsa ya bayyana. Ku yi kwaxai Allah ya jiqan ku! Ku yi taimakekeniya a bisa biyayya da tsoron Allah. Ku kevanci talakawa daga makusantanku da zakkarku, domin zakkarka gare su ninki biyu ce. Sadaka da sa da zumunci. Ka bincika maqotanka, ku yi taimakon juna a wjen binciken talakawa da waxanda suka cancanta don biyayya ga Allah, da neman kusanci da shi zuwa ga Allah.

Ina roqon Allah Ya karvi kyawawan ayyuka daga gare mu da ku, shi Mai iko ne a bisa kowane abu. Ku sani Allah Ya jiqan ku, mafi kyawun zanci shi ne littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya, shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ).